Rikicin Rivers: Tsohon Shugaban PDP Ya Fadi Dalilin Takun Sakar Wike da Gwamna Fubara

Rikicin Rivers: Tsohon Shugaban PDP Ya Fadi Dalilin Takun Sakar Wike da Gwamna Fubara

  • Tsohon shugaban jam’iyyar PDP, Prince Uche Secondus, ya yi zargin cewa Nyesom Wike, na kitsa rikicin siyasa a jihar Rivers ne saboda ƙin bari a saci dukiyar jihar da Gwamna Siminalayi Fubara ya yi
  • Uche Secondus ya soki salon mulkin Wike lokacin da yake gwamnan Rivers inda ya yi zargin cewa tsohon gwamnan ya jawo taɓarɓarewar tattalin arziƙin jihar
  • Jigon na PDP ya yi kira ga shugaban ƙasa Bola Tinubu da ya sa baki domin hana ɓarkewar rikicin siyasa a jihar ta yankin Kudu maso Kudu

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Prince Uche Secondus, tsohon shugaban jam’iyyar PDP na ƙasa, ya ce ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, shi ne ke kitsa rikicin siyasar da Gwamna Siminalayi Fubura ke fama da shi.

Kara karanta wannan

PDP ta sake samun nakasu bayan tsohon kakakin majalisa ya fice daga jam'iyyar

Tsohon shugaban na jam’iyyar PDP, ya bayyana hakan ne a birnin tarayya Abuja a ranar Asabar, 11 ga watan Mayun 2024.

Uche Secondus ya caccaki Wike
Uche Secondus ya fadi dalilin rikicin siyasar Rivers Hoto: @SimFubaraKSC, @micah_egele, @GovWike
Asali: Twitter

Ya bayyana cewa abokan hamayyar Gwamna Fubara sun taso shi a gaba ne saboda ya ƙi yarda a dasa wawa kan dukiyar jihar, cewar rahoton jaridar Vanguard.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewar tsohon shugaban na PDP, rikicin siyasar jihar Rivers ya samo asali ne daga masu neman a ba su dama su yi watanda da dukiyar jihar, wanda Gwamna Fubara ya ƙi amincewa da hakan.

'Wike ya ɓata sunan Rivers' - Secondus

Da yake ƙarin haske, Uche Secondus ya ce kalaman da Wike yake yi da takun saƙarsa da gwamnan ya ɓata sunan jihar.

Jigon na PDP ya ce Wike lokacin da ya yi gwamna, ya lalata tattalin arziƙin jihar Rivers saboda munanan tsare-tsarensa.

Kara karanta wannan

Ganduje da APC sun yi rashi, dubunnan mambobin jam'iyyar sun koma NNPP

Ya ce ministan na babban birnin tarayya Abuja ya kasa jawo wani aiki daga gwamnatin tarayya zuwa jihar Rivers tun da ya ɗare kan kujerar.

"Wike ya yi gwamna na tsawon shekara takwas kuma yanzu ya zama ministan babban birnin tarayya Abuja. A matsayinsa na minista wane aiki ya samo daga gwamnatin tarayya zuwa Rivers. Wataƙila sai dai baƙin ciki da damuwa."
"A lokacin da yake gwamna ya jawo ficewar masu zuba hannun jari saboda munanan tsare-tsarensa."
"Ya taɓa ambaton cewa yana iya haddasa rikici kuma hakan ba ƙarya ya yi ba, domin yana jawo gagarumin rikici a jihar Rivers."

- Prince Uche Secondus

Rikicin Rivers ya ɗauki sabon salo

A wani labarin kuma, kun ji cewa rikicin siyasar jihar Rivers ya sauya salo bayan rantsar da sabon kakakin majalisar dokokin jihar mai biyayya ga Gwamna Fubara.

An naɗa Victor Oko Jumbo wanda ke wakiltar mazabar Bony a jihar Rivers a matsayin shugaban tsagi na majalisar bayan an yi barazanar tsige gwamnan jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng