Alaranma Yayi Tonon Silili, Ya Fallasa Yadda Aka Saye Malamai a 2027 Aka Rufe Masu Baki

Alaranma Yayi Tonon Silili, Ya Fallasa Yadda Aka Saye Malamai a 2027 Aka Rufe Masu Baki

  • Ismail Maiduguri ya zargi wasu daga cikin malaman musulunci da kiristanci da biyewa ‘yan siyasa lokacin zabe
  • Malamin Al-Kur’anin ya ce yawan cikan sahu a masallatai da coci ake amfani da su a wajen sayen bakin malamai
  • Gwani Ismail Maiduguri ya ce tun da an karbi kudin ‘yan siyasa, dole yanzu ba za a iya kokawa da irin mulkinsu ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abuja - Ismail Maiduguri ya tofa albarkacin bakinsa game da halin da Najeriya take ciki a karkashin jagorancin Bola Ahmed Tinubu.

Alhafiz Ismail Maiduguri ya ce a yanzu ‘yan siyasa sun fahimci cewa za a iya yin amfani da abin duniya a saye kuri’u lokacin zabe.

Ismail Maiduguri
Ismail Maiduguri ya ce an saye malamai Hoto: Ismail Maiduguri/@Dolusegun (X)
Asali: UGC

"An saye malamai" - Ismail Maiduguri

Wani bidiyon malamin a shafin X ya nuna shi yana bayanin yadda aka yi amfani da taliya wajen samun goyon bayan talaka a bara.

Kara karanta wannan

Matakai 5 da Gwamnatin Tinubu ta dauka da suka jefa ‘yan Najeriya a wahalar rayuwa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Baya ga talakawa, ya ce masu mulkin yau sun yi amfani da dukiyarsu wajen rufa bakin wasu malaman addinin musulunci da kirista.

Akwai malamai na Allah a Najeriya

Wannan malami ya ce ba a taru an zama daya ba, amma akwai jagororin addini da suka cefanar da matsayin da Ubangiji ya ba su.

"Akwai malamanku da fastoci da ke cewa a zabi wane da kyakkyawar niyya. Amma akwai da yawa da ciniki ake yi da su."
"Iyakar yawan masu yi masa (malami) kabbara ko halleluiah a coci, iya yawan kudin da za a ba shi (Fasto, Fada ko Rabaren)."

- Ismail Maiduguri

Malamai sun karbi kudi sun yi gum?

Ismail Maiduguri ya yi ikirarin bayan zabe ba a jin wani ya fito ya ce uffan saboda kudi ne suka yi aiki wajen samun shugabanci.

Kara karanta wannan

InnalilLahi: 'Yan bindiga sun bindige ma'aikacin FIRS a tsakiyar birnin Abuja

Malamin yake cewa ko da farashin man fetur ya tashi, sai dai a ji masana addini suna fadawa talaka ya kara hakuri kuma ya tuba.

A ina malamin ya yi karatun nan?

Bayanan sun zo ne a wajen karatun littafin da ya fara game da tarihin mata da mazan da ka kewaye da Annabi Muhammad SAW.

Sa’ad Yusuf Abu Azeez ya rubuta fitaccen litafin da malamin yake karantarwa a masallacin Zone B a rukunin gidajen ‘yan majalisu.

Sai dai Ismail Maiduguri yana ganin akwai laifin talaka domin ba tursasa masa aka yi, shi da kan shi ya zabi wadanda aka tallata masa.

Malamin musulunci ya yi kira ga Tinubu

An ji labari babban malamin nan, Sheikh Adamu Muhammad Dokoro ya ce talakawa suna shan wahala a gwamnatin APC mai-mulki.

Adamu Muhammad Dokoro yana so shugabanni su gama lafiya, ba wai su gama da talakawansu ba ganin ana cikin kuncin rayuwa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng