Barau, Ndume da Sauran Sanatoci da Ka Iya Rasa Kujerunsu Kan Babban Kuskure
- Kungiyar ALDRAP ta maka wasu mambobin Majalisar Dattawa kusan 40 a gaban babbar kotun Tarayya da ke Abuja
- Kungiyar ta na kalubantar sanatocin ne kan rike mukamai a mabambantan Majalisu da suka hada da na ECOWAS da Pan-African
- Daga cikin wadanda suka shiga matsala akwai mataimakin shugaban Majalisar, Barau Jibrin da Ali Ndume da Smart Adeyemi da sauransu
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Mambobin Majalisar Dattawa akalla 40 ne ka iya rasa kujerunsu ciki har da mataimakin shugaban Majalisar, Sanata Barau Jibrin.
Duk da kasancewarsu a Majalisar Tarayyar Najeria suna kuma da rike da kujeru a Majalisar ECOWAS da kuma ta Pan-African.
Sanatocin da ka iya rasa kujerunsu
Bayan sanata Barau wanda shi ne ke rike da mukamin mukaddashin shugaban Majalisar akwai sanata Ali Ndume, cewar Premium Times.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sauran sun hada da Smart Adeyemi da Mshelia Haruna da Abiodun Olujimi da Tolu Odebiyi da sauransu.
Wannan na zuwa ne bayan maka 'yan majalisun a Babbar Kotun Tarayyar da cibiyar ALDRAP ta yi.
ALDRAP na neman tabbatar da gaskiya da bin diddigi kan dukkan al'amuran shugabanci ba tare da kwana-kwana ba.
Sakon kungiyar ga Akpabio kan sanatocin
Kungiyar ta bukaci shugaban Majalisar, Godswill Akpabio ya rusa kujerunsu saboda rike mukamai a mabanbantan Majalisu tare da karbar alawus.
Bayan Akpabio ya gagara daukar wani mataki kan wannan lamari, kungiyar ta dauki matakin shiga kotu.
Kungiyar ta yi barazanar a cikin wata takarda da sakatarenta, Tonye Clinton Jaja ya sanyawa hannu a ranar 8 ga watan Afrilun wannan shekara.
Har ila yau, kungiyar ta ce kasancewarsu a majalisu biyu ya saba doka sashe na 68 na kundin tsarin mulkin 1999.
Majalisa ta dauki mataki kan safarar kwayoyi
A wani labarin, Majalisar Tarayya ta amince da dokar hukuncin kisa kan masu safarar kwayoyi a fadin ƙasar.
Majalisar ta amince da hakan ne bayan kai ruwa rana game da matakin yayin zaman Majalisar tsakanin mambobinta.
Sanata Adams Oshiomole ya kalubalanci dokar inda ya ce ba a gaggawa kan irin wannan da ya shafi rai da rayuwar ɗan Adam.
Asali: Legit.ng