“An Kara Albashin Sanatoci, ‘Yan Majalisa Daga N13m da N21m Zuwa N8.5m da N13m”
- Ja’afar Ja’afar ya fito yana zargin cewa an yi wa duk wani ‘dan majalisar tarayya da sanata karin albashin da yake karba
- ‘Dan jaridar ya fito yana ikirarin sanatan da ake biya N13.5m a kowane wata, yana tashi da sama da N20m a halin yanzu
- Idan zancen Ja’afar gaskiya ce, ‘yan majalisar wakilan tarayyan kasar sun samu karin miliyoyin kudi a kan albashinsu
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.
Abuja - Fitaccen ‘dan jaridar nan, Ja’afar Ja’afar ya yi ikirarin an kara albashin da ‘yan majalisar tarayya suke karba.
Malam Ja’afar Ja’afar ya yi wannan magana ne a shafukansa na sada zumunta musamman a X da kuma Facebook.
Ana jiran Tinubu ya kara albashin ma'aikata
‘Dan jaridar ya tada kuri’a, ya jawo ana ta tir da gwamnatin Bola Tinubu a lokacin da mutane ke jiran a kara albashin ma’aikata.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Da yake magana a dandalin X, Ja’afar ya ce idan za a cire tallafi ko kara kudin lantarki, farat daya ake yanke hukunci.
Amma idan ana bukatar karin albashi, ya ce sai a yi ta zaman kwamitoci barkatai har da yajin-aiki kafin a waiwayi ma’aikata.
"An kara albashin 'yan majalisa" - Ja'afar
“A karkashin shugaban kasa (Bola) Tinubu, kowane Sanata ya samu karin albashi daga N13.5m zuwa N21m a kowane wata
Kamar yadda albashin ‘yan majalisar wakilan tarayya ya karu daga N8.5, zuwa N13.5m.
Nawa ne sabon mafi karancin albashin da ma’aikatan gwamnati suke karba?”
- Ja'afar Ja'afar
Mutane sun soki 'karin' albashin 'yan majalisa
Fateema Muhammad Bawa ta ce:
"Taliya ce Sanadi"
“Allah Sarki talaka”
Inji Alhaji Muhammad Mardy
“Kai dai Nigeria sai dai mu ci gaba da addu'a.. amma wahalan ba ta misaltuwa”
- Kabir Easer
Auwal Ubangida Dunari yake cewa:
“Allah ya saka mana mun shiga hannun 'yan sari”
Auwal Salisu Isah yana mamakin ganin yadda gwamnatin tarayya ta gaza yanke N150, 000 a matsayin mafi karancin albashi.
Wani Malam Ghali ya ce:
"Abin takaici."
"A jihar Borno kuwa, wasu malaman N7500 su ke karba," a cewar Halilu Abdullahi.
Shi kuwa wani Prince D. Biechiey sai dai ya yi ta salati:
“Innalillahi wa inna ilaihi raji'un”
Nazifin Jarumi Rurum kuwa ya goyi bayan karin albashin, ya ce:
“Sune suke dawainiya da al'ummar, ai kudinmu wajensu yake komawa kacokan gaba daya, fatanmu Allah yakawo mana dauki”
Sanatoci da 'yan majalisa za su ci N50bn
Rahoto ya zo a baya cewa albashi da alawus na duka ‘Yan majalisar Najeriya a tsawon shekaru hudu yana neman kai N50bn.
Nan da 2027, ‘Yan majalisar wakilai da Sanatocin tarayya za su raba Naira biliyan 32 tsakaninsu alhali ana biyan ma'aikata N30, 000.
Asali: Legit.ng