Shugaban PDP Ya Fadi Jihar da Jam'iyyar Za Ta Kwace a Hannun APC

Shugaban PDP Ya Fadi Jihar da Jam'iyyar Za Ta Kwace a Hannun APC

  • Shugaban jam'iyyar PDP na ƙasa ya yi magana kan zaɓen gwamnan jihar Ondo da za a gudanar a watan Nuwamban 2024 da ke tafe
  • Ambassada Umar Damagum ya bayyana cewa jam'iyyar ta shirya ƙwace jihar a hannun abokiyar hamayyarta APC mai mulki
  • Ya kuma yi wa jam'iyyar APC shaguɓe kan yadda ta gudanar da zaɓen fidda gwanin gwamnanta cike da ruɗani

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Muƙaddashin shugaban jam’iyyar PDP na ƙasa, Ambasada Umar Damagum, ya ce jam’iyyar a shirye take ta lashe zaɓen gwamnan jihar Ondo da za a yi a watan Nuwamba.

Hakan na zuwa ne yayin da ya yi kira ga ɗan takarar jam’iyyar, Alfred Agboola Ajayi, da ya yi aiki tare da sauran ƴan takarar domin tabbatar da nasarar jam’iyyar.

Kara karanta wannan

Ondo: Jam'iyyar APC za ta bayar da satifiket din lashe zaben fidda gwani

PDP ta shirya kwace jihar Ondo
Shugaban PDP ya ce jam'iyyar ta shirya karbe jihar Ondo a hannun APC Hoto: All Progressives Congress, Peoples Democratic Party
Asali: Facebook

Ya bayyana hakan ne a lokacin da yake jawabi ga masu ruwa da tsaki na jam’iyyar gabanin gabatar da takardar shaidar lashe zaɓen fidda gwanin gwamna ga Alfred a hedikwatar jam’iyyar da ke Abuja, cewar rahoton Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An yi wa jam'iyyar APC shaguɓe

Umar Damagum ya kuma yi wa jam'iyyar APC mai mulki shaguɓe kan yadda ta gudanar da zaben fidda gwaninta cike da ruɗani.

"A lokacin da abokan hamayyarmu suka kasa haɗa kansu wuri ɗaya, mu ƴan adawa mun kunyata su, mun fitar da ɗan takara ba tare da nuna adawa ba."
"A yayin taron masu ruwa da tsaki, mun amince cewa dukkanin ƴan takara daga Kudu za su fito, kuma cikin yardar Allah abin da ya faru kenan. Hakan ya nuna a shirye yake mu karɓe jihar Ondo."
"Ko a zaɓen da ya gabata, mun san cewa jihar Ondo ta PDP ce, kuma bayan tattaunawa da masu ruwa da tsaki mun fitar da ɗan takara ɗaya."

Kara karanta wannan

Malam El-Rufai zai kara da Tinubu a zaben shugaban ƙasa a 2027? Gaskiya ta bayyana

- Umar Damagum

An ba ɗan takarar PDP shawara

Ya gayawa ɗan takarar kada ya yi wasa da cewa dukkanin abokan takararsa sun yadda da kayen da ya yi musu, rahoton Daily Post ya tabbatar.

A kalamansa:

"Kana buƙatar ƙara dagewa domin tafiya tare da su ta yadda zaka samu nasara. Kammala wannan aikin shi ne lashe jihar Ondo domin PDP. Ba abu ba ne mai sauki, sai ka fara tun daga farko."

APC za ta iya rasa mulkin Ondo?

A wani labarin kuma, kun ji cewa wani jigo a jam’iyyar APC, Bamidele Oloyeloogun, ya bayyana damuwarsa kan cewa jam’iyya za ta iya yin rashin nasara a zaɓen gwamnan jihar mai zuwa.

Bamidele Oloyeloogun ya yi nuni da da cewa APC ka iya yin rashin nasarar ne idan ba a soke zaɓen fidda gwani na gwamna da ta yi ba a jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng