Tsohon Dan Takarar Shugaban Kasa Ya Fice Daga Jam'iyyar PDP
- Tsohon dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar PDP a zaben 2023, Cosmos Ndukwe, ya sanar da ficewarsa daga PDP
- Mista Ndukwe ya bayyana haka ne a yau Litinin cikin wata budaddiyar wasika da ya wallafa a shafinsa na Facebook
- Duk da cewa bai bayyana jam'iyyar da zai koma ba, ya tura sako na musamman ga jam'iyyar PDP da ya bari
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Abia - Tsohon shugaban ma'aikatan Abia kuma tsohon kwamishinan ayyuka na jihar, Cosmos Ndukwe ya fice daga jam'iyyar PDP.
Mista Ndukwe ya yi godiya ga jam'iyyar bisa damar da ta ba shi ya haska tauraronsa na siyasa a shekarun baya.
Tsohon dan takarar shugaban kasan ya bayyana haka ne a cikin wata wasika da ya wallafa a shafinsa na Facebook a yau Litinin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Dalilin fitan Cosmos Ndukwe daga PDP
A cikin wasikar, ya bayyana cewa barin jam'iyyar yana da alaka da wasu dalilai na karan kansa da kuma wasu lamura da sune masu muhimmanci a gare shi a halin yanzu.
Ya kara da cewa jam'iyyar ta masa komai tunda ta ba shi damar rike mukamai da dama cikin shekarun da yake cikinta.
Matsayin da Ndukwe ya rike a PDP
Ya ce jam'iyyar ta ba shi damar zama daga kansila har dan takarar shugaban kasa a shekarar 2023.
Saboda haka ya yi godiya ga dukkan 'ya'yan jam'iyyar bisa karamcin da aka yi masa cikin shekaru.
'Dan siyasar ya kuma kara da cewa bayan fita daga jam'iyyar ba wai karshen sa a siyasa ba kenan, ya ce zai cigaba da iya kokarinsa wurin kawo cigaba ga damokradiyya da jihar Abia.
A karshe ya kuma yi fatan alheri da samun nasara ga jam'iyyar PDP a faɗin jihar dama Najeriya baki daya.
An dakatar da shugaban PDP a Ondo
A wani rahoton, kun ji cewa kwamitin gudanarwa na ƙasa (NWC) na jam’iyyar PDP ya yi watsi da batun dakatar da shugaban jam’iyyar na jihar Ondo, Fatai Adams
Kakakin jam’iyyar PDP, Debo Ologunagba, a wata sanarwa da ya fitar ranar Talata, ya ce dakatarwar ta saɓawa kundin tsarin mulkin jam’iyyar da ƙa’idojin jam’iyyar
Asali: Legit.ng