Manyan Yan Takarar Shugaban Kasa 5 Da abinda Ya Kamata Ka Sani Dangane Da Su

Manyan Yan Takarar Shugaban Kasa 5 Da abinda Ya Kamata Ka Sani Dangane Da Su

  • Yan takara guda biyar sune wanda zakaransu yai cara da za’a iya cewa a tsakaninsu ne za’a samu wanda zai lashe takarar shugaban kasar Nigeria
  • Kowanne cikin yan takarar ya ja zare, tare da shirin danbatawa a filin damben yakin neman darewa kan kujerar
  • Masana, masu sharhin yau da kullum na ganin wadannan giwayen sune zasu kai batansu zuwa zuwa ga akwatunan zabe tare da samun nasara

Nigeria – Hausawa sukance idan giwaye biyu na fada, ciyawar wajence take jin jiki. To ina ga giwaye biyar da suka hadu a waje daya suke neman abu guda.

Batu ne na babban zaben Nigeria da za’a gabatar a watan gobe da jibi, wato Faberu da kuma maris, dan zabar wanda zai dare shugabancin kasar nan tsowon shekara hudu.

Kara karanta wannan

Indai So Ake A Magance Matsalar Tsaro Da Satar Dukiyar Kasa To Atiku Ne zai Iya Magance Su, Tambuwal

Manyan yan takara da ake tunanin zasu maye gurbin shugaba buharin sun hada Major Hamza Al-mustapha mai ritaya da Alhaji Atiku Abubakar Daga yankin arewa maso gabashin Nigeria.

Sai tsohon gwamnan jihar kano kuma tsohon sanatan kano ta tsakiya Alhaji Rabi’u Musa Kwankwaso daga yankin arewa maso yamma.

Shi kuma Peter Obi ya fito ne daga yankin kudu masu gabashin kasar nan yayin da abokin burminsa ya fito daga yankin kudu maso yamma Nigeria.

1. Atiku Abubakar na jam'iyyar PDP

Mai shekara 75 a duniya, ya rike mataimakin shugaban kasar Nigeria daga shekarun 1999-2006, kuma an taba zabarsa sa gwamnan jiharb adamawa a zaben 1999.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Yayi aiki da hukumar shige da ficen Nigeria wato Custom, sannan rikakken dan kasuwa ne da ya shawara wajen kasuwanci da hada-hadar kamfanunuwa.

Kara karanta wannan

2023: Mata Za Su Samu Kudi a Karkashin Gwamnatin Mijina, In ji Matar Obi

Yayi takara shugabancin Nigeria karo hudu, inda ya fara da shekarar 2007, hatta a zaben da ya gabata na 2019 ma yayiwa jam’iyyar PDP takara.

Atiku nada goyan bayan gwamnoni masu ci guda goma sha daya, yayin da yake samu sabani da wasu gwamnonin jam’iyyarsa guda biyar da suka kira kansu da G-5.

Akwai has ashen cewa Atiku kan iya cin wasu jihohi daga yankin arewa maso gabas, Kaman Adamawa Jiharsa da Taraba da hasashe mai karfi kan lashe jihohin Bauchi da gombe.

Haka zalika mai yiwuwa ya lashe jihohin sokoto da Jigawa a rewa maso gabas da kuma samu wasu kuri’un masu yawa a jihohin Kaduna. Haka ma a jihohin tsakaiyra Nigeria akwai has ashen lashe jihohin Benue, Pleatue da kuma jihar Kwara inda tsohon shugaban majalisar dattijai yake.

Atiku
Manyan Yan Takarar Shugaban Kasa 5 Da abinda Ya Kamata Ka Sani Dangane Da Su Hoto: Vanguard
Asali: UGC

Haka jihohin Osun da oyo na daga cikin jihohin kudancin kasar nan na Kudu maso yamma da ake has ashen dan takarar zai lashe. Akwai jihohin Rivers, Cross-Rivers, Delta AKwa-Ibom Enugu daga yankin kudu maso kudu da kudu maso gabas da ake tunanin dan takarar ya lashe.

Kara karanta wannan

2023: Tsohuwar Minista Ta Tsoma Baki, Ta Tona Asirin Mai Hana Ruwa Gudu a Rigingimun PDP

Atiku ne dai na gaba-gaba wajen ganin ya lashe wannan takarar domin itace damar sa ta karshe.

2. Bola Ahmed Tinubu

Dan shekara 70 a duniya wanda ya fito daga yankin yarabawa Nigeria, Tinubu na da goyan bayan gwamnonin APC gaba dayansu tare da yan majalisar wakilai da dattijai.

Tinubu wanda yake tsohon ma'aikacin kamfanunuwa a ciki da wajen Nigeria farwa da wani kamfani a kasar Amurka zuwa kasar Ingila da kuma gida Nigeria.

Ya zama gwamnan jihar Lagos a 1999 zuwa 2006 inda ya bunkasa tare da habaka yaransa na Siyasa a lokacin.

Tinubu na takama da goyan bayan gwamnonin jam'iyyar APC kafataninsu harda wanda sukai takara ko iuma suka janye masa, haka zalika Tinubu na takama da goyan bayan yan majalissun tarayya dana dattijai.

Takarar dai Musulmi da Musulmi da Tinubun ya dauko ta samu tagomashi na cikas da yabo daga wajen dai-daiku da gwamman kungiyoyi.

Kara karanta wannan

2022: Wasu manyan abubuwa 10 da suka faru a 2022, sun ja hankalin jama'a a duniya

3. Hamza Almustapha Na AA

Dan shekarar sittin da biyu, tsohon soja, tsohon dogarin shugaban kasa a mulkin soja Janr Sani Abacha.

Za'a a iya cewa kusan rayuwar Al-mustapha ta kare ne kwacokan a aikin soja sai kuma gidan yarin da ya zauna tsahon shekara goma sha uku.

Da yawa daga cikin matasan Nigeria na goyan bayan Hamza sabida yadda yake nunawa matasan gobensu a kusa, a hirarraki da ya yawa da akeyi dashi ana jin yadda Hamza ke ambatar hanyoyi, dabaru da wasu hikimomi da za'ai amfani da su wajen raya kasa da matasa.

Hamza
Manyan Yan Takarar Shugaban Kasa 5 Da abinda Ya Kamata Ka Sani Dangane Da Su Hoto: Facebbok
Asali: Facebook

Dan jihar Yobe da jam'iyyar APC ke mulki yayi takara a karo na biyu kenan inda yake takara a jam'iyyar AA wadda ko dan majalissa bata da shi, amma ana ganin mutane na yawan magana akan dan takarar shugaban kasarta.

4. Rabiu Kwankwaso Na NNPP

Kara karanta wannan

WAsu Abubuwa Da Zasu Faru Wanda Baza Su Sake Faruwa Ba A Irin Wannan Yanayin

Dan shekara 65 a duniya wanda ya kasance tsohon gwamnan jihar Kano, tsohon ministan tsaron Nigeria, tsohon sanatan Kano ta tsakiya kuma tsohon shugaban hukumar kula da tafkin Chadi.

Rabi'i Kwankwaso na takama da goyan bayan kanawa da kuma hausawa da suke arewa maso yamma (Inda yake gidansu) da kuma hausawa da suke zaune a yankin Kudu maso gabas, yamma da kudu maso kudu.

Rabi'u Kwankwaso
Manyan Yan Takarar Shugaban Kasa 5 Da abinda Ya Kamata Ka Sani Dangane Da Su Hoto: Kwankwaso
Asali: UGC

Ana masa ikirari da "Local Champion" ma'ana wanda iya a yankinsa aka sanshi. Kwankwaso ya dauko jam'iyyar NNPP wanda kafin lokacin ya shiga bata da ko dan majalissa jiha, amma yanzu akwai yan majalissun tarayya dana dattijai da kuma wasu jiga-jigan siyasa a Nigeria da jihohi.

5. Peter Obi Na LP

Magoya bayansa na wa kansu kirara da "Obedient". Peter Obi wanda ya fito daga Jihar Anambra wadda take kudu maso gabashin Nigeria, kuma yai mata gwamna tsahon shekara takwas.

Kara karanta wannan

Tashin Hankali: 'Yan Bindiga Sun Yi Wa Shugaban Jam'iyyar PDP Yankan Rago a Jihar Arewa

Peter Obi dan kasuwane kuma dan siyasa ne, yayiwa Alhaji Atiku Abubakar takarar mataimakin shugaban kasa a kakar zaben shekarar 2019.

Rashin adalicin da ya kira da jam'iyyar PDP tai masa ne yasa ya bar jam'iyyar kuma ya koma jam'iyyar LP sannan kuma ya zama dan takarar shugaban kasa.

Ana ganin Peter Obi zai bada ruwa sosai a yankin da ya fito da kuma wasu yankunan kudu maso yammacin kasar nan.

Peter
Manyan Yan Takarar Shugaban Kasa 5 Da abinda Ya Kamata Ka Sani Dangane Da Su Hoto: Vanguard
Asali: UGC

Zabe

A ranar 25 ga watan Fabairun wannan shekarar za'a kada kuri'ar zaben shugaban kasa a duk fadin Nigeria, wanda hukumar zaben Nigeria ta ke shiryawa kuma ta gabatar karkashin shugabanta na yanzu da kwamishinoninsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel