Uba Sani v El-Rufai da Jerin Gwamnatoci Masu Mulki da ke Binciken Gwamnonin Baya

Uba Sani v El-Rufai da Jerin Gwamnatoci Masu Mulki da ke Binciken Gwamnonin Baya

Nigeria - Wasu sababbin gwamnoni da wadanda suke wa’adi na biyu suna binciken gwamnatocin da suka shude a jihohinsu.

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Legit ta kawo jerin jihohin da gwamnatoci masu-ci suke kokarin bibiyar abubuwan da suka faru kafin su shiga ofis a 2019 ko 2023.

Gwamnoni
Gwamnoni na binciken magabatansu a Najeriya Hoto: @KYusufAbba, @AAdeleke_01, @UbaSaniUS
Asali: UGC

Jihohin da ake binciken tsofaffin gwamnoni

1. Kaduna

Majalisar dokokin Kaduna ta fara binciken bashi da harkokin kudi da suka gudana a lokacin da Malam Nasir El-Rufai ya yi gwamna.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hakan ya biyo bayan korafin da Uba Sani ya yi na cewa an bar masa bashi a Kaduna.

2. Kano

Gwamnatin Abba Kabir Yusuf tana binciken Abdullahi Umar Ganduje da gwamnatinsa, an kafa kwamitoci domin yin wannan aiki a Kano.

Kara karanta wannan

Gwamnonin Arewa sun bayyana dalilansu na zuwa Amurka taron zaman lafiya

Ana zargin gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje da rashin gaskiya da yin bakar siyasa.

3. Sokoto

Tun tuni gwamnatin Sokoto ta sanar da cewa an kafa kwamiti da zai binciki kadarorin gwamnati da Aminu Tambuwal ya saida a mulkinsa.

Binciken gwamna Ahmed Aliyu ya shafi nadin mukamai a gwamnatin Tambuwal, saida filaye, dukiyoyi da sauran gidajen gwamnatin Sokoto.

4. Kuros Riba

Shi ma Mai girma Bassey Otu ya kafa kwamiti da zai binciki gwanjon kadarori da Ben Ayade ya yi a sa’ilin da yake gwamna a Kuros Ribas.

5. Nasarawa

Kamar a Kaduna, majalisar dokokin jihar Nasarawa ta kafa kwamiti na musamman da zai binciki ayyukan gwamnatin Tanko Umar Al-Makura.

Kwamitin zai duba yadda aka saida wasu gidajen gwamnatin Nasarawa da ke Legas.

6. Benuwai

Hyacinth Alia yana zama gwamna ya taso Samuel Ortom wanda ya yi mulki tsakanin 2015 da 203 da binciken yadda ya cefanar da kadarori.

Ana duba yadda aka yi gwanjon kamfanoni, kasuwanni da sauran arzikin jihar Benuwai.

Kara karanta wannan

"Ku daina tsoma baki a gwamnatina" Gwamna ya gargaɗi tsofaffin gwamnoni

7. Osun

Shi kuwa Ademola Adeleke ya nada kwamiti domin duba yadda gwamnatin Adegboyega Oyetola ta ba da kwangiloli kafin ya karbi mulki.

8. Taraba

Shi ma Agbu Kefas yana da kwamiti da yake duba ayyukan ma’aikatu da hukumomin gwamnatin Taraba tun daga 2019 har zuwa 2023.

9. Zamfara

Shi ma Dauda Lawal ya na binciken Bello Mattawalle, har ya zarge shi da yin gaba da wasu motocin gwamnatin Zamfara da zai bar ofis a bara.

Jihohin da APC ba ta gwamna a Najeriya

Ku na da rahoto cewa daga 1999 har zuwa yau, akwai wasu jihohin da har gobe PDP ce ta rike da su a matakin gwamna ba duk zaben da ake yi.

Jam'iyyar PDP ta yi tashe musamman saboda yin shekaru 16 a jere tana kan karagar mulki kuma ba ta taba fadi zaben gwamna a jihar Ribas ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng