Binciken Ganduje: Kungiya Ta Ja Kunnen Abba Kabir, Ta Fadi Babbar Matsalarsa

Binciken Ganduje: Kungiya Ta Ja Kunnen Abba Kabir, Ta Fadi Babbar Matsalarsa

  • Kungiyar Arewa Renaissance Front ta dauki zafi kan binciken Abdullahi Ganduje da ake shirin yi a Kano
  • Kungiyar ta bukaci Gwamna Abba Kabir na Kano da ya janye kudirinsa na binciken tsohon gwamnan jihar
  • Wannan na zuwa ne yayin da gwamnan ya kafa kwamitin bincike kan zargin badakalar kadarorin gwamnatin jihar

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kano - Kungiyar Arewa Renaissance Front (ARF) a Kano ta gargadi Gwamna Abba Kabir kan binciken Abdullahi Umar Ganduje.

Kungiyar ta bukaci gwamnan ya dakatar shirin binciken inda ta ce hakan bita da kullin siyasa ne kawai, cewar Tribune.

Kungiya ta shawarci Abba Kabir kan binciken Ganduje
Kungiyar ARF ta bukaci Gwamna Abba Kabir ya janye shirin binciken Umar Ganduje. Hoto: @OfficialAPCNg, @Kyusufabba.
Asali: Twitter

Wane zargin kungiyar ta yi kan Abba?

Kara karanta wannan

Abduljabbar: ’Yan sanda sun bankado shirin kungiyoyin addini da siyasa domin rikita Kano

ARF ta kuma zargi gwamnan da neman kawar da hankalin jama'a kan rashin iya jagoranci inda ya ke neman tayar da maganar binciken.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da babban sakataren kungiyar, Aminu Gawama ya fitar a yau Laraba 10 ga watan Afrilu, cewar The Guardian.

"Mu a Arewa Renaissance Front muna sane bita da kullin siyasa da ake yi kan shugaban jam'iyyar APC, Abdullahi Ganduje."

- Aminu Gawama

Ta gano shirin Abba kan binciken Ganduje

"Mun fahimci takun gwamnan Kano wurin neman kawar da hankalin jama'a yayin da ya gagara tabuka wani abin a zo a gani a jihar."
"Jama'ar Kano na tambaya, mene gwamnan ya yi a jihar tun bayan hawansa mulki fiye da shekara daya duk da yawan kudade da ya ke samu daga Gwamnatin Tarayya?."

- Aminu Gawama

Kara karanta wannan

"Za mu waiwayi bidiyon dala": Abba ya magantu kan shekara 8 na mulkin Ganduje a Kano

Kungiyar ta ce Ganduje ba ya tsoron wani bincike saboda duk abin da ya aikata lokacin da ya ke gwamnan jihar a bayyane su ke.

APC ta ba Abba shawara kan Ganduje

A wani labarin, mun ruwaito muku cewa jam'iyyar APC a Kano ta shawarci Gwamna Abba Kabir kan binciken shugaban jam'iyyar, Abdullahi Ganduje.

Jam'iyyar ta ce ya kamata gwamnan ya fara binciken tsohon gwamnan jihar, Sanata Rabiu Kwankwaso kan badakalar da ya tafka.

Hakan ya biyo bayan kafa kwamitin bincike da gwamnan ya yi kan zargin siyar da kadarorin gwamnati a jihar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel