Bola Tinubu Ya Yi Sababbin Naɗe-Naɗe a Muhimman Hukumomi 2 Na Ƙasa
- Bola Ahmed Tinubu ya naɗa shugabannin da za su jagoranci wasu hukumomin gwamnatin tarayya guda biyu ranar Jumu'a
- Shugaban ya naɗa Dokta Innocent Bariate Barikor a matsayin shugaban hukumar NESREA da Prince Ebitimi Amgbare a matsayin shugaban NDRBDA
- Mai magana da yawun shugaban ƙasa, Ajuri Ngelale ne ya sanar da haka a wata sanarwa da ya fitar ranar Jumu'a, 26 ga watan Afrilu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
FCT Abuja - Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya nada Dokta Innocent Bariate Barikor a matsayin Darakta-Janar na Hukumar Kula da Muhalli ta Kasa (NESREA).
Shugaban ƙasar ya kuma nada Prince Ebitimi Amgbare a matsayin manajan darakta/Shugaba na hukumar raya kogin Neja Delta (NDRBDA).
Waɗannan muhimman naɗe-naɗe na kunshe ne a wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun mai magana da yawun shugaban ƙasa, Ajuri Ngelale ranar Jumu'a.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Mai taimakawa shugaban ƙasa na musamman kan harkokin kafafen sadarwa na zamani, Olusegun Dada, ya wallafa sanarwar naɗe-naɗen a shafinsata na manhajar X.
A cewar sanarwar, Dr Barikor ya kasance mamban majalisar dokokin jihar Ribas daga shekarar 2011 zuwa 2015.
Y.ayin da Prince Amgbare, tsohon jami’in rundunar sojan ruwa ne wanda ya yi ritaya kuma tsohon kwamishina a jihar Bayelsa.
Tinubu ya masu fatan alheri
Kakakin shugaba Tinubu ya ce ana sa ran Dr. Barikor da Prince Amgbare za su sauke nauyin da ya rataya a wuyansu tare da yin ayyuka masu kyau da hidima ga al’ummar Najeriya.
"Shugaban ƙasa yana sa ran sabbin shugabannin wadannan muhimman hukumomi za su yi aikinsu cikin rikon amana ga al'ummar kasa.
"Yana fatan za su yi amfani da kwarewa, rikon amana, domin yin kyakkyawar hidima ga al'ummar Najeriya."
- Ajuri Ngelale.
Tinubu ya naɗa shugaban NELFund
A wani rahoton kuma Shugaba Bola Tinubu ya nada wanda ya kafa bankin Zenith, Jim Ovia, a matsayin shugaban hukumar bayar da lamunin ilimi ta Najeriya.
Mai magana da yawun shugaban kasar, Ajuri Ngelale, ya fitar da sanarwar wannan nadin a ranar Juma'a, 26 ga watan Afilu.
Asali: Legit.ng