Binciken Ganduje: IGP Ya Janye Ƴan Sanda Daga Hukumar PCACC Ta Jihar Kano

Binciken Ganduje: IGP Ya Janye Ƴan Sanda Daga Hukumar PCACC Ta Jihar Kano

  • Ana zargin babban sufetan ƴan sanda na ƙasa (IGP), Kayode Egbetokun ya janye jami'an yan sanda daga hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta Kano
  • A cewar wata majiya daga hukumar, ƴan sandan da aka ɗauke suna taimakawa a manyan bincike ciki har da na shugaban APC, Abdullahi Ganduje
  • Majiyar ta koka kan cewa shugaban rundunar ƴan sandan, wanda ya janye ƴan sanda daga wurin Yahaya Bello, ya ƙara tsaurara tsaron Ganduje

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Kano - Sufetan ƴan sanda na ƙasa, IGP Kayode Egbetokun, ya janye ƴan sanda 40 dake aikin tsaro da bincike a hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta Kano.

Ana zargin IGP ya ɗauki wannan matakin ne sakamakon binciken cin hanci da rashawa da hukumar ke yi wa shugaban jam'iyyar APC na ƙasa, Abdullahi Ganduje.

Kara karanta wannan

Masu kantin da ya hana 'yan Najeriya sayayya sun amsa gayyatar hukumar FCCPC

Ganduje da Gwamna Abba.
An zargin rundunar ƴan sanda ta janye dakarunta daga hukumar yaki da rashawa ta Kano Hoto: Dr. Abdullahi Umar Ganduje, Abba Kabir Yusuf
Asali: Twitter

Meyasa IGP ya ɗauke ƴan sandan?

A cewar rahoton Daily Nigerian, sufetan ƴan sandan ya ba da umarnin janye ƴan sandan ga kwamishinan ƴan sanda na jihar Kano, Usaini Gumel ranar Alhamis.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wata majiya daga hukumar ta bayyana cewa ƴan sandan da aka janye suna taimakawa sosai a manya-manyan binciken cin hanci da rashawa.

Sannan suna ba da tsaro a hedkwatar hukumar yaƙi da cin hanci ta Kano (PCACC) da wasu muhimman kayayyaki da aka kwace, rahoton Solabase.

Majiyar ta koka da cewa ofishin hukumar da ke binciken shugaban jam’iyyar APC mai mulki na ƙasa kuma tsohon gwamnan jihar a yanzu yana cikin rauni.

Majiyar ta ce:

"Abin ɗaure kai shi ne rundunar ƴan sandan da ta janye jami'anta daga jikin tsohon gwamnan Kogi, Yahaya Bello, ta kuma koma ta tsaurara tsaro a jikin Ganduje domin hana a cafke shi.

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun cafke mutum 2 masu safarar makamai ga 'yan bindiga a jihar Kaduna

"Bayan haka, a yanzu kuma sun janye tsaro daga hukumar yaki da cin hanci da rashawa.”

Abdullahi Ganduje da gwamnatin Kano

A baya-bayan nan Ganduje ya zargi gwamnatin Kano da hannu a shirya dakatar da shi daga APC amma ba a daɗe ba kotun da ta tsige shi ta sake maida shi.

Tun da ya sauka daga kujerar gwamna, sabuwar gwamnati ta lashi takobin binciko gaskiyar da ke tattare da bidiyon 'Dalar' da ake zargin Ganduje da cin hanci.

Ganduje ya samu goyon baya a APC

A wani rahoton shugabannin jam'iyyar APC na jihohi sun kaɗa kuri'ar amincewa da Dakta Abdullahi Umar Ganduje a matsayin shugaban jam'iyyar na ƙasa.

Sun tabbatar da wannan matsaya ne yayin da suka ziyarci babbar sakatariyar APC ta ƙasa da ke birnin tarayya Abuja ranar Talata.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262