Rahoton Amurka Ya Fallasa Yadda Aka Yi Amfani da Addini da Kabilanci a Zaben 2023
- Kasar Amurka ta fitar da rahoto na musamman a kan yadda babban zaɓen shekarar 2023 ya gudana a Najeriya
- A cewar rahoton za a iya cewa mutane sun samu abin da suka zaba amma an tafka kura-kurai da dama cikin zaben
- Ya kuma bayyana yadda aka yi amfani da addini da kafafen sadarwa wurin dakile mata 'yan siyasa a zaben
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Kasar Amurka ta fitar da rahoto na musamman a kan kurakurai da aka tafka a babban zaben Najeriya da ya gabata a shekarar 2023.
Duk da cewa zaben ya bar baya da kura, a cewar rahoton za a iya cewa masu zabe sun samu abin da suka zaba a wurare da dama.
A rahoton da kasar ta fitar a shafin yanar gizonta, ya nuna cewa an samu kura-kurai da dama a zaben ciki har da sayen kuri'a, tashin hankali da barazana ga masu zabe
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Zaben 2023: Abin da ya faru a Legas
Rahotan ya bada misalin abin da ya faru a Legas na nuna kabilanci ga magoya bayan dan takarar jami'yyar Labour, Peter Obi.
A cewar rahoton, magoya bayan jam'iyyar APC sun yi barazana ga 'yan ƙabilar Ibo a yankunan da Peter Obi ya lashe zabe a jihar Legas.
Ya kuma kara tabbatar da cewa an samu shedar faifayin bidiyo a kafafen sada zumunta da ya ke nuna magoya bayan APC na barazana ga magoya bayan jam'iyyar Labour a yankin Ojo.
Ta kara da cewa an samu irin barazanar a yankin Eti-Osa da Amuwo-Odofin kuma an samu inda magoya bayan APC su ka kai hari wa 'yan jarida.
Har ila yau, a cikin faifayin bidiyon akwai shedar cewa 'yan sanda na wurin amma ba a dauki mataki ba kuma ba a kama masu laifin daga baya ba.
Yadda aka dakile mata a zaben 2023
Rahoton ya kuma nuna yadda aka ware mata a harkar zaben ta inda ya kasance mata kadan ne suka samu yin nasara a kujerun da suka nema.
A cewar rahoton, matsalolin addini, al'adu da tattalin arziki sun yi tasiri sosai wurin rashin samun nasarar mata a zaben.
Ya kara da cewa an yi amfani da kafafen sadarwa wurin dakile mata ta inda wasu kafafen suka ki tallata mata 'yan siyasa.
Amurka ta gargadi Isra'ila kan yaki da Iran
A wani rahoton kuma, kun ji cewa kasar Amurka ta gargadi Isra'ila a kan yin amfani da karfin soja wurin kai harin ramako zuwa Iran
Amurka ta yi gargadin ne saboda a cewarta barkewar yaki tsakanin ƙasashen zai haifar da yaki mai muni a yankin gabas ta tsakiya.
Asali: Legit.ng