Dakatar da Ganduje: Alkalin Kotun Kano Ya Warware Hukuncin da Ya Yi a Kan APC
- Babbar kotun jihar Kano ta warware hukuncin da ta yi a ranar 17 ga watan Afrilu na dakatar da Abdullahi Ganduje daga jam'iyyar APC mai mulki
- Alkalin kotun, Usman Mallam Na'abba wanda ya yanke hukuncin ya ce Ganduje zai ci gaba da zama a jam'iyyar yayin da ake ci gaba da shari'ar
- A makon baya Legit Hausa ta ruwaito cewa wani Haladu Gwanjo da Laminu Barguna ne suka nemi kotun da ta dakatar da Ganduje daga APC
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Kano - Alkalin babbar kotun jihar Kano, Mai shari'a Usman Mallam Na'abba ya yi watsi da wani hukunci na kotun da ta yi na dakatar da Abdullahi Ganduje daga jam'iyyar APC.
Idan ba a manta ba, Mai shari'a Na'abba ne dai ya yanke hukuncin dakatar da Ganduje daga jam'iyyar a 17 ga watan Afrilu 2024.
Kotu ta janye umarnin dakatar da Ganduje
A hukuncin da kotun ta yanke a yau Litinin, 22 ga watan Afrilu, Mai shari'a Na'abba ya warware wancan hukuncin da ya yi, kamar yadda sanarwar da Legit ta samu ta nuna.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sanarwar ta ce wani Haladu Gwanjo da Laminu Sani Barguna ne suka nemi kotun ta dakatar da Ganduje daga shugaban jam'iyyar, rokon da alkalin ya amince da shi.
A lokacin, Haladu da Laminu sun yi ikirarin cewa su ne shugaba da sakataren APC a gundumar Ganduje da ke karamar hukumar Dawakin Tofa.
Sai dai, sanarwar ta ce Mai shari'a Na'abba ya yanke hukunci na watsi da wancan umarnin na farko bayan karbar korafi na shafuka 27 daga wata Glory Adah, sakatariya a jam'iyyar APC ta reshen Kano.
Ganduje: Hukuncin da alkalin kotun ya yanke
Sanarwar ta ce:
"Bayan jin ta bakin Mr. L. O. Oyewo Esq, tare da A. Falana Esq da J. Essiet Esq, lauyoyin jam'iyyar APC reshen Kano, wannan kotu ta warware umarninta na dakatar da Ganduje daga APC."
Kotun ta ce wannan sabon hukunci na nufin Abdullahi Ganduje wanda ake kara na hudu zai ci gaba da zama a jam'iyyar APC har zuwa lokacin yanke hukunci na karshe.
Alkalin kotun sai ya dage sauraron shari'ar zuwa ranar 30 ga watan Afrilu a domin fara sauraron jawaban bangarorin da abin ya shafa.
Za a iya tsige Ganduje kamar Oshiomhole?
A wani labarin, sakataren yada labarai na jam'iyyar APC, Felix Morka ya ce yanayin da ya sa aka dakatar da Adams Oshiomhole daga shugaban jam'iyyar ya sha bamban da na Abdullahi Ganduje.
Morka ya yi nuni da cewa dukkanin wadanda ke hankoron dakatar da Ganduje ba halastattaun 'yayan jam'iyyar ba ne, sabanin Oshiomhole kuwa shugabannin APC ne suka kore shi.
Asali: Legit.ng