Kano: Takaddama Yayin da Tsagin APC Ya Sake Dakatar da Ganduje Kan Wasu Sabbin Dalillai

Kano: Takaddama Yayin da Tsagin APC Ya Sake Dakatar da Ganduje Kan Wasu Sabbin Dalillai

Wani tsagin jam'iyyar APC a gundumar Ganduje ya sake tabbatar da korar Abdullahi Ganduje daga jam'iyyar

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kano - Sabuwar takaddama yayin da tsagin jam'iyyar APC a matakin unguwa ya sake dakatar da Abdullahi Ganduje a jami'yyar.

Jam'iyyar ta dauki matakin ne bayan wani tsagin jam'iyyar a Ganduje da ke karamar hukumar Dawakin Tofa ya musanta dakatar da Ganduje.

Wani tsagin APC ya sake dakatar da Ganduje daga kujerarsa
Tsagin jam'iyyar APC a Kano ya tabbatar da dakatar da Abdullahi Ganduje. Hoto: Abdullahi Umar Ganduje.
Asali: Facebook

Yadda aka sanar da dakatar da Ganduje

Yayin da ya ke zantawa da manema labarai, sakataren jam'iyyar a Unguwar Ganduje, Ja'afar Adamu Ganduje ya ce sun dauki matakin ne a madadin masu ruwa da tsakin jam'iyyar 11.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kara karanta wannan

Matsalar tsaro ta ta'azzara a Filato, an rufe jami'ar jihar bayan kashe dalibi

Ja'afar ya ce sun dakatar da tsohon gwamnan ne kan zargin cin dunduniyar jami'yyar da ya jawo mata rashin nasara a zaben 2023.

Ya ce cin amanar jami'yyar da ya yi ya jawo rashin nasara musamman a zaben jihar Kano da aka gudanar, cewar The Guardian.

Adamu wanda ɗan uwa ne ga Ganduje ya ce ayyukan tsohon gwamnan ya kawo rikici a jami'yyar da ke neman wargaza ta.

Ya kuma zargi Ganduje da rashin biyan kudin jam'iyyar wanda hakan ya sabawa dokar jami'yyar, cewar Premium Times.

Musabbabin dakatar da Ganduje daga APC

"Mune ainihin shugabannin jam'iyyar APC a gundumar Ganduje, kuma bamu tare da Ganduje, mun sake dakatar da shi kan wasu dalilai da dama."
"Na farko, mun dakatar da shi saboda kawo rikici a jam'iyya tsakanin mambonin jam'iyyar a matakin unguwa."
"Wani babban dalili kuma shi ne cin dunduniyar jam'iyyar da ya yi a zaben 2023 wanda ya yi sanadin rashin nasararta a jiha."

Kara karanta wannan

Za a iya tsige Ganduje daga ofis kamar Oshiomhole? APC ta yi karin haske

- Ja'afar Adamu

Sakataren jam'iyyar ya ce dukkan wadancan bangarori guda biyu da ke cewa sune shugabannin jam'iyyar ba gaskiya suke ba kuma na bogi ne.

APC ta ayyana zaben fidda gwani 'inconclusive'

Kun ji cewa, jam'iyyar APC a jihar Ondo ta ayyana zaben fidda gwani da ake gudanarwa wanda bai kammala ba.

Shugaban kwamitin zaben, Gwamna Usman Ododo na jihar Kogi shi ya tabbatar da haka inda ya ce an samu matsaloli.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.