Jihohi 5 da Mulkinsu Bai Taba Barin Hannun Jam’iyyar PDP ba a Tsawon Shekara 25
Abuja - Kamar yadda akwai wasu jerin jihohin da PDP ba ta taba mulkarsu ba, akwai wadanda mulkinsu bai subucewa jam’iyyar ba.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.
A rahoton nan, mun kawo jihohin da jam’iyyar PDP zalla kadai ta mulke su tun daga lokacin da aka shigo jamhuriyya ta hudu a 1999.
Jihohin da PDP ta rike tun 1999:
1. Akwa Ibom
Daga 1999 zuwa zaben karshe da aka yi bara, jam’iyyar PDP kurum ta ke lashe zaben gwamnan jihar Akwa Ibom da ke Kudu maso kudu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tun daga Victor Attah, Godswill Akpabio har zuwa Umo Eno, duk sun yi mulki ne a PDP duk da Akpabio yana cikin jiga-jigan APC a yau.
2. Delta
Babu wata jam’iyya da ta iya kafa gwamna a Delta sai PDP; James Ibori, Emmanuel Uduaghan, Ifeanyi Okowa har zuwa Sheriff Oborevwori.
Tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawa, Ovie Omo-Agege ya nemi karye tarihin a APC a zaben 2023, Sheriff Oborevwori ya doke shi.
3. Bayelsa
Diepreye Alamieyeseigha, Goodluck Jonathan, Timipre Sylva, Seriake Dickson da Douye Diri sun yi mulki ko suna mulkin Bayelsa ne a PDP.
A zaben 2020, APC ta lashe zaben gwamna amma kotu ta soke nasarar David Lyon saboda badakalar takardu, a haka PDP ta cigaba da mulki.
4. Enugu
A tsawon shekarun nan 25, mutanen jihar Enugu ba su san kowace jam’iyya a zaben gwamna ba face babbar jam’iyyar hamayya ta PDP.
Chimoroke Nnamani, Sullivian Chime, Ifeanyi Ugwuanyi sun yi mulki ne a PDP yanzu kuma Peter Mbah yake rike da ragamar Enugu.
5. Taraba
Taraba ce kadai jihar Arewa da take hannun jam’iyyar PDP tun 1999. Jam’iyyar NNPP ta yi hobbasa a 2023, sai dai ta kare a ta biyu a takarar.
Gwamnonin jihar a tarihin farar hula su ne: Jolly Nyame, Danbaba Suntai, Garba Umar, Sani Danladi, Darius Ishaku sai Kefas Agbu a yau.
Sauran jihohin PDP a Najeriya
Wata Jihar Kudu maso kudancin Najeriya ita ce Ribas wanda tun da ake farar hula jam’iyyar PDP ce ta ke lashe zaben gwamna.
A 2013, Rotimi Amaechi ya sauya-sheka zuwa APC, zuwa 2015 PDP ta karbe iko.
APC ba ta taba rike Abia ba, amma PPA ta karbe jihar kafin gwamna Theodore Orji ya sauya sheka, a yau Alex Otti da LP ne da iko.
Jihohin da PDP ba ta mulka ba
Wannan rahoto ya nuna Legas tana cikin jihohin da sai dai jam'iyyar PDP ta gansu kuma dole ta bar su a tarihin mulkin farar hula.
Jam’iyyar PDP ba ta taba cin zaben Zamfara ba, amma ta kafa gwamnati sau biyu lokacin Mahmud Shinkafi da Bello Matawalle.
Asali: Legit.ng