"Allah Kaɗai Ke Ba da Mulki," Atiku Ya Mayar da Martani Kan Zargin Cin Amana a Taron NEC

"Allah Kaɗai Ke Ba da Mulki," Atiku Ya Mayar da Martani Kan Zargin Cin Amana a Taron NEC

  • Alhaji Atiku Abubakar ya jaddada cewa babu wani mahaluƙi daga cikin ƴan Adam da ke bayar da mulki sai dai Allah maɗaukakin Sarki
  • Tsohon mataimakin shugaban kasar ya faɗi haka ne yayin da wasu magoya bayansa suka fara zargin mambobin PDP sun ci amanarsa a taron NEC
  • Sau 6 Atiku ya yi takara domin zama shugaban ƙasa a Najeriya amma bai taɓa samun nasara ba

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya bayyana cewa babu wani dan Adam da zai iya ba da mulki sai Allah Madaukakin Sarki.

Kalaman Atiku na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da cece-kuce biyo kan sakamakon taron kwamitin zartarwa na jam’iyyar PDP na kasa karo na 98 wanda aka yi a Abuja.

Kara karanta wannan

Taron NEC: Babban jigo ya buƙaci shugaban PDP na ƙasa ya yi murabus nan take

Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar.
Atiku Abubakar ya mayar da martani kan taron NEC bayan raɗe-raɗin an ci amanarsa Hoto: Atiku Abubakar
Asali: Getty Images

Ɗan takarar shugaban kasa na PDP a zaɓen 2023 ya faɗi haka ne a cikin wata tattaunawa ta WhatsApp da wasu magoya bayansa a kasar nan ranar Juma'a.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Matakan da PDP ta ɗauka a NEC

A cewar kakakin PDP, Debo Ologunagba, daga cikin matakan da jam'iyyar ta ɗauka a taron ranar Alhamis har da sake fasalin kwamitin ladabtarwa.

Haka zalika PDP za ta sake duba kwamitin sulhu domin tabbatar da zaman lafiya a cikin gida, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

Daga cikin muhimman hukunce-hukuncen da aka yanke a taron NEC, jam’iyyar ta kuma nada tsohon gwamnan jihar Akwa Ibom, Emmanuel Udom, a matsayin shugaban kwamitin ladabtarwa.

Sannan kuma tsohon shugaban majalisar dattawa, Sanata Bukola Saraki, zai ci gaba da riƙe shugabancin kwamitin sulhu da sasanci.

Allah kaɗai ke bayar da mulki

Kara karanta wannan

Mulkin Tinubu ya dara shekaru 16 a PDP ta fuskar tsaro, Hadimin Tinubu

Amma Atiku ya shaida wa magoya bayansa a manhajar WhatsApp bayan taron NEC cewa Allah ne kadai ke bada mulki.

Martanin nasa ya biyo bayan zage-zagen da magoya bayansa ke yi na cewa wasu ‘yan jam’iyyar sun ci amanar sa.

Tsohon mataimakin shugaban kasar, wanda ya yi takarar zama shugaban Najeriya sau shida amma bai ci ba, ya ce, “Akwai Allah. Allah ne kaɗai ke ba da mulki ba wani mahaluƙi ba.

Wani.jigon PDP kuma masoyin Atiku a jihar Katsina, Kabir Abdullahi, ya shaida wa Legit Hausa cewa ko kaɗan ba su ji daɗin abin da aka yi a taron NEC ba.

A cewarsa alamu sun nuna manyan PDP da gwammnoni sun fara juyawa tsohon mataimakin shugaban kasar baya amma hakan ba zai girgiza shi ba.

Ɗan siyasar ya ce:

"Mu a wurin mu bamu ji daɗin taron nan ba domin an fara juya mana baya, amma na san Atiku ya saba fuskantar irin haka, misali abin da ya faru a zaben fitar da gwani a 2019.

Kara karanta wannan

'Bam' da ƴan ta'adda suka dasa ya halaka bayin Allah sama da 10 a Arewacin Najeriya

"Duk da bamu ji daɗi ba, mun san Atiku zai nemo mafita, kamar yadda ya faɗa mulki na Allah ne kuma shi ke bayar wa ga wanda ya so kuma a lokacin da ya so, nan ne matsayar mu."

Ganduje na nan a shugaban APC

A wani rahoton kuma Jam'iyyar APC ta jaddada cewa Dakta Abdullahi Umar Ganduje na nan daram a matsayinsa na shugaban jam'iyyar na ƙasa.

Mai magana da yawun APC, Felix Morka, ya ce ba za su yi aiki da umarnin kotun farko ba, amma suna tare da hukuncin babbar kotun tarayya

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262