Mulkin Kano: An Buƙaci EFCC Ta Gudanar da Bincike Tare da Gurfanar da Kwankwaso
- Mai yiwuwa jagoran Kwankwasiyya, Rabiu Musa Kwankwaso ya shiga komar binciken EFCC kan wa'adin mulkinsa a Kano
- Wasu ƙungiyoyin fararen hula 45 sun roki EFCC ta binciki jagoran NNPP domin tabbatar da haƙikanin yadda ya sarrafa dukiyar al'umma a mulkinsa
- Kwankwaso dai ya mulki Kano na tsawon zango biyu a lokuta daban-daban, 1999 zuwa 2003 da kuma 2011 zuwa 2015
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Kano - Ƙungiyoyin fararen hula 45 sun rubuta wasiƙa zuwa ga hukumar yaƙi da masu yi wa tattalin arziki zagon ƙasa (EFCC) domin ta binciki Rabiu Kwankwaso.
Kungiyoyin karƙashin ƙungiyar fafutukar tabbatar da adalci ga kowa (JA) sun buƙaci EFCC ta bude shafin binciken wa'adin Kwankwaso a kujerar gwamnan Kano, rahoton Leadership.
Rabiu Kwankwaso, jagoran New Nigeria Peoples Party (NNPP), ya mulki Kano a lokuta daban-daban, wa'adin farko daga 1999 zuwa 2003 da kuma na biyu daga 2011 zuwa 2015.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
JA ta buƙaci a titsiye Kwankwaso ne a wasiƙar da ta aike wa EFCC mai ɗauke da sa hannun shugabanninta, Auwalu Ibrahim da Dave Ogbole a madaɗin ƙungiyoyi 45.
Meyasa suka nemi a binciki Kwankwaso?
A cewarsu, wannan binciken ya zama wajibi domin ganin an bi kadin dukiyar jihar Kano bisa la’akari da halin kuncin da al’ummar jihar ke ciki wanda ba a taba ganin irinsa ba.
Wasiƙar kungiyoyin ta yi bayanin cewa bincikar Kwankwaso zai cike gibin da ke akwai na tabbatar da yaki da cin hanci da rashawa a gwamnatocin da suka shuɗe.
Bugu da ƙari ta nuna yadda kananan hukumomi suka karɓi kason N107.29bn daga gwamnatin tarayya a 2015 amma babu wani abu da aka yi da kuɗin da za ka nuna a yanzu.
"Gwamnatin Abdullahi Ganduje da ta shude ta gaza yin bincike kan zamanin Kwankwaso, haka nan ma gwamnatin Abba Yusuf mai-ci ba ta da niyyar yin hakan."
Kwankwaso da Hukumar EFCC
Kungiyar JA ta bukaci hukumar EFCC da ta yi duk abin da ya dace don ganin gwamnatin Kwankwaso ta yi bayanin yadda aka sarrafa dukiyar jihar Kano a lokacin wa'adinta.
A baya dai EFCC ta taɓa fara binciken Kwankwaso kan zargin almundahana a lokacin mulkinsa, kamar yadda Premium Times ta ruwaito.
Dagaske NNPP ta dakatar da Abba?
Rahoto ya zo cewa jam'iyyar NNPP ƙarƙashin jagorancin Ahmed Ajuji ta musanta dakatar da gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf.
Muƙaddashin shugaban NNPP na ƙasa ya ce waɗanda suka dakatar da Abba Kabir ƴan barkwancin siyasa ne da ke neman suna.
Asali: Legit.ng