'Babu Wanda Zai Shigo APC sai da Izinin Ganduje,' An Ja Kunnen Kwankwasiyya

'Babu Wanda Zai Shigo APC sai da Izinin Ganduje,' An Ja Kunnen Kwankwasiyya

  • Jam'iyyar APC ta ce babu wanda ya isa ya shigo cikinta har sai Abdullai Umar Ganduje ya sahale tare da sa masa albarka
  • Kakakin jam'iyyar a Kano, Ahmed S Aruwa ne ya shaidawa Legit Hausa hakan, inda ya ce fadar shugaban kasa na kaunar Ganduje
  • Jawabin na a matsayin martani kan rahoton cewa ya aibata fadar shugaban kasa da kokarin cire Ganduje daga mukaminsa.

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Kano -Jam'iyyar APC a Kano ta ce babu wanda zai shiga jam'iyyar face Shugabanta, Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya sa masa albarka.

Kakakin jam'iyyar a Kano, Ahmed S Aruwa ne ya shaidawa Legit Hausa hakan a yammacin Alhamis.

Kara karanta wannan

Jam'iyyar APC ta yi magana kan umarnin kotu, ta faɗi mutanen da suka dakatar da Ganduje

kakakin APC na Kano, Ahmed S Aruwa
Ahmed S Aruwa ya ce rikicin da ke faruwa da Ganduje a APC makircin Kwankwasiyya ne Hoto: Ahmad Aruwa
Asali: Facebook

Alakar Ganduje da Shugaba Tinubu a APC

'Dan siyasar ya bayyana cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu na kaunar Dr. Ganduje, kuma babu wanda zai taba alakarsu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Da yake magana ka labarin yana zargin gwamnatin tarayya da kokarin tunbuke Dr. Ganduje daga mukaminsa, Ahmed S Aruwa ya ce sharri ne irin na 'yan adawa, domin suna biyayya ga fadar shugaban kasar.

"Wannan kalma ce kawai ta 'yan adawanmu da muke da ita a nan Kano."

- Ahmad Aruwa

Ya ce labarin da ake yayatawa ya dade sosai, wanda yana magana ne kan jagoran kwankwasiyya dake kokarin hada kai da wasu a fadar shugaban kasa domin yi wa shugabansa zagon kasa.

Kwankwaso da mutanensa na son dawowa APC?

Ahmed S Aruwa ya zargi jagoran NNPP, Injiniya Rabi'u Musa Kwankwaso da kunno wutar rikici a jam'iyyar APC saboda baya son zama inuwa guda da Ganduje a shirinsa na dawowa jami'iyyar.

Kara karanta wannan

Dakatar da Ganduje: Jam'iyyar APC ta mayar da martani kan hukuncin babbar kotun Kano

Ya ce:

"Mun je mun yi bincike mun gane 'yan kwankwasiyya ne, mutanen NNPP ne."
"Kuma mun kai kara, kuma mun turawa 'yan sanda, mun turawa daraktan tsaro, in Allah SWT ya yarda wadannan yaran, za a kamo su, za a kai su gaban kuliya."

Kakakin APCn ya ce ba su bukatar Kwankwaso da jama'arsa su dawo APC matukar rikici za su taho da shi.

"Babu mai iya jinjigani," Dr. Ganduje

Tun bayan dambarwar da ta faro da ayyana korar tsohon Gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje daga jam'iyyar APC ne shugaban ke ganin babu mai iya jijjiga shi.

A sakon da ya tura ga 'yan adawa, Dr. Ganduje ya bayyana cewa ya riga ya sha gabansu, saboda haka magana ce kawai ake amma babu abin da zai taba kujerarsa ta shugabancin jam'iyyar APC ta kasa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.