El-Rufai: Majalisar Dokokin Kaduna Ta Ja Kunnen Bello El-Rufai, Ta Fadi Matsayarsa Kan Binciken

El-Rufai: Majalisar Dokokin Kaduna Ta Ja Kunnen Bello El-Rufai, Ta Fadi Matsayarsa Kan Binciken

  • Yayin da ake tababa kan zargin gwamnatin Nasir El-Rufai, Majalisar jihar Kaduna ta gargadi Bello El-Rufai
  • Kakakin Majalisar, Hon. Yusuf Liman shi ya yi wannan gargadi inda ya ce ɗan tsohon gwamnan ya na musu barazana
  • Wannan na zuwa ne yayin da Majalisar jihar ke shirin binciken gwamnatin El-Rufai kan badakalar kudi a jihar

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kaduna - Kakakin Majalisar jihar Kaduna, Hon. Yusuf Liman ya gargadi, Bello El-Rufai kan barazanar da ya ke yi musj.

Liman ya ce ɗan tsohon gwamnan jihar, Nasir El-Rufai ya na yi masa barazana da Majalisar kan binciken mulkin mahaifinsa.

Majalisa ta gargadi Bello El-Rufai kan barazana da ya ke mata
Majalisar dokokin jihar Kaduna ta gargadi ɗan tsohon gwamnan jihar, Bello El-Rufai kan barazanar da ya ke mata. Hoto: @B_ELRUFAI.
Asali: Twitter

Wane zargi Majalisar ke yi kan El-Rufai?

Kara karanta wannan

Tsohon kakakin Majalisa ya jefa El-Rufai a matsala, ya faɗi gaskiya kan bashin $350m

Kakakin Majalisar ya ce Bello ya tura masa sakwannin barazana da cin mutunci wanda yanzu ya goge su a dandalin X da kuma dandalin Whatsapp kan binciken gwamnatin Nasir El-Rufai.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da hadiminsa, Suraj Bamalli ya fitar a shafin Facebook a yau Laraba 17 ga watan Afrilu.

"Duk wata barazana daga kowa ciki har da mambobin Majalisar Tarayya ba zai hana Majalisar gudanar da aikinta na tabbatar da gaskiya ba."
"Majalisar tana kan bakanta na tabbatar da bincike da bin diddigi domin tabbatar da bin dokokin jihar Kaduna."
"Kan wannan lamari, Majalisar jihar Kaduna ta na gargadin Bello El-Rufai kan irin wannan rashin da'a da ya ke nunawa."

- Suraj Bamalli

Majalisa ta shawarci al'ummar jihar Kaduna

Sanarwar ta koka kan yadda ɗan Majalisar Tarayya da ke wakiltar jama'a zai rinka aikata irin wannan rashin tarbiyya.

Kara karanta wannan

Binciken El-Rufai: An bayyana dalilin kafa kwamitin bin diddikin ayyukan tsohon gwamnan

Majalisar ta kuma bukaci al'ummar jihar da su saka ido tare da tabbatar da ba da goyon baya domin bin gaskiya da adalci.

Ta kara da cewa akwai hujjojin dukkan abubuwan da Bello El-Rufai ya fada wanda aka adana su domin zama shaida.

"Zulum ya fi kowa aiki", El-Rufai

Kun ji cewa tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya bayyana gwamnan da ya fi kowa aiki a duk fadin Najeriya.

El-Rufai ya zabi gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum a matsayin gwamnan da ya fi jajircewa kan ayyukansa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel