Tsohon Kakakin Majalisa Ya Jefa El-Rufai a Matsala, Ya Faɗi Gaskiya Kan Bashin $350m

Tsohon Kakakin Majalisa Ya Jefa El-Rufai a Matsala, Ya Faɗi Gaskiya Kan Bashin $350m

  • Yayin da Majalisar jihar Kaduna ta kafa kwamitin binciken Nasir El-Rufai, tsohon kakakin Majalisar ya kare kansa
  • Yusuf Zailani ya karyata cewa ya amince da bashin $350m ga gwamnatin Nasir El-Rufai yayin shugabancinsa a Majalisar
  • Wannan na zuwa ne bayan Majalisar jihar ta kafa kwamitin binciken tsohuwar gwamnatin jihar Kaduna daga 2015-2023

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kaduna - Tsohon kakakin Majalisar jihar Kaduna, Yusuf Zailani ya yi martani kan zargin amincewa da bashin $350m.

Yusuf Zailani ya ƙaryata amincewa da bashin makudan kudi ga tsohon gwamnan jihar, Nasir El-Rufai daga Bankin Duniya.

Tsohon kakakin Majalisar Kaduna ya fede gaskiya kan bashin $350m ga El-Rufai
Tsohon kakakin Majalisar Kaduna, Yusuf Zailani ya yi magana kan amincewa da bashin $350m ga Nasir El-Rufai. Hoto: @elrufai.
Asali: Twitter

Dalilin kafa kwamitin binciken El-Rufai

Wannan ya biyo bayan kafa kwamitin bincike kan gwamnatin El-Rufai daga shekarar 2015 zuwa 2023 da Majalisar ta yi.

Kara karanta wannan

El-Rufai: Majalisar dokokin Kaduna ta ja kunnen Bello El-Rufai, ta fadi matsayarsa kan binciken

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yayin da ya ke kare kansa, tsohon kakakin Majalisar ya ce bai amince da bashin ba yayin da ya ke shugabancin Majalisar.

Hadimin kakakin Majalisar, Suraj Bamalli shi ya wallafa faifan bidiyo inda Zailani ke kare kansa a Majalisar jihar.

"Na dade ina jiran wannan rana, wasu mambobin Majalisar suna wurin, shida daga cikinsu har yanzu mambobin wannan Majalisar ne."
"Cikinsu har da tsohon mataimakin shugaban Majalisar, Isaac Auta Zankhai, sun ce na amince da bashin amma na na ƙi, na ce ya kamata mu san bashin nawa muke da shi."

- Yusuf Zailani

Bincike: Wane mataki Majalisar Kaduna ta ɗauka?

Majalisar ta kuma bukaci a gayyato tsofaffin kakakin Majalisar na takwas da kuma na tara da tsohon kwamishinan kudi.

Sauran sun hada da daraktoci a ma'aikatu da kwamishinan kasafin kudi da tsare-tsare da sauran masu da riƙe da manyan mukamai.

Kara karanta wannan

Binciken El-Rufai: An bayyana dalilin kafa kwamitin bin diddikin ayyukan tsohon gwamnan

Majalisar Kaduna ta gargadi Bello El-Rufai

A wani labarin, Majalisar jihar Kaduna ta tura sakon gargadi ga ɗan tsohon gwamnan jihar Kaduna, Bello El-Rufai.

Majalisar na zargin Bello da tura mata sakon barazana da kuma kakakin Majalisar, Yusuf Liman kan binciken da Majalisar ta kafa kan Nasir El-Rufai.

Hakan ya biyo bayan zargin da Gwamna Uba Sani ya yi kan tulin bashi da tsohon gwamnan ya bar masa a gwamnanti.

Asali: Legit.ng

Online view pixel