Dakatar da Ganduje: Daga Karshe An Bayyana Wadanda Suka 'Kitsa' Shirin

Dakatar da Ganduje: Daga Karshe An Bayyana Wadanda Suka 'Kitsa' Shirin

  • Shugabannin jam'iyyar APC na ƙaramar hukumar Dawakin Tofa sun musanta sun tsame kansu daga batun dakatarwar da aka yi wa Abdullahi Umar Ganduje
  • Mai ba jam'iyyar shawara kan harkokin shari'a na ƙaramar hukumar, Halliru Gwanzo, shi ne ya bayyana hakan a birnin tarayya Abuja
  • Ya yi nuni da cewa sojan gona aka yi masa wajen sanar da dakatarwar inda ya zargi gwamnatin NNPP da ƴan Kwankwasiyya kan kitsa shirin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Shugabannin jam’iyyar APC reshen ƙaramar hukumar Dawakin Tofa a jihar Kano, sun musanta cewa suna da hannu wajen dakatar da shugaban jam’iyyar na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje.

Shugabannin sun bayyana hakan ne a ranar Laraba bayan sun ziyarci sakatariyar jam'iyyar APC a birnin tarayya Abuja.

Kara karanta wannan

Dakatar da Ganduje: Jam'iyyar APC ta mayar da martani kan hukuncin babbar kotun Kano

Shugabannin APC sun musanta dakatar da Ganduje
Shugabannin APC sun musanta masaniya a dakatar da Ganduje Hoto: Dr. Abdullahi Umar Ganduje - OFR
Asali: Facebook

TABLE OF CONTENTS

APC ta musanta dakatar da Ganduje

Mai ba jam'iyyar shawara kan harkokin shari’a a Dawakin Tofa, Halliru Gwanzo, ya musanta hannunsu a cikin dakatarwar a Abuja, cewar rahoton jaridar The Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwanzo dai ya jagoranci tawagar mutane 27 da suka kai ziyarar nuna goyon baya ga Ganduje a sakatariyar jam’iyyar APC da ke Abuja.

'Dan siyasar ya kuma ce bai san komai ba game da ƙarar da aka shigar a kotu a kan tsohon gwamnan na jihar Kano, rahoton The Eagle ya tabbatar.

Hakan dai na zuwa ne kwanaki biyu bayan da ɗan siyasar ya shaida wa manema labarai a Kano cewa, shugabannin jam’iyyar APC na mazaɓar ne suka ɗauki matakin dakatar da tsohon gwamnan.

Wa ke da hannu a dakatar da Ganduje

Da yake yi wa manema labarai jawabi a ranar Laraba a Abuja, Gwanzo, wanda ya yi iƙirarin cewa sojan gona aka yi masa, ya roƙi jam’iyya mai mulki da ta binciki lamarin tare da hukunta waɗanda duk aka samu da laifi.

Kara karanta wannan

Kotu ta dauki mataki kan dakatarwar da aka yi wa Ganduje daga jam'iyyar APC

"Ina nan a yau tare da mambobi 27 daga mazaɓarmu da ke ƙaramar hukumar Dawakin Tofa a Jihar Kano don shaida wa duniya cewa ba mu san komai ba game da batun dakatar da shugabanmu na ƙasa. Ba gaskiya bane."
"Na yi mamaki, kamar kowane mutum, da na sake ganin sunana a matsayin ɗaya daga cikin waɗanda suka kai ƙararsa da safiyar yau. Ƙarya ce tsagwaronta."
"Ban san komai ba game da waɗannan zarge-zarge, kuma ina amfani da wannan damar wajen yin kira ga shugabannin babbar jam’iyyarmu da kuma kwamitin ayyuka na kasa da su bi kadin masu yin sojan gonan."
"Bai kamata a kyale su ba. Mun san gwamnatin NNPP ce da ƴan Kwankwasiyya ne suka shirya hakan.”

- Halliru Gwanzo

Ganduje ya aika saƙo ga gwamnatin Kano

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban jam'iyyar APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje, ya aika da saƙo ga gwamnatin jihar Kano.

Ganduje ya shaidawa Gwamna Abba Yusuf cewa shi yanzu ya zama turmi sha daka kuma bishiyar kuka da babu mai iya jijjiga shi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng