Babban Jigon APC Ya Aike da Saƙo Ga Ƴan Majalisar Tarayya 60 da Ke Shirin Sauya Sheƙa

Babban Jigon APC Ya Aike da Saƙo Ga Ƴan Majalisar Tarayya 60 da Ke Shirin Sauya Sheƙa

  • Jigon APC ya buƙaci ƴan majalisar tarayya 60 da suka yi barazanar ficewa daga jam'iyyar PDP da su sauya tunani
  • Ƴan majalisun sun gindaya sharaɗin cewa matukar Umar Damagum ya ci gaba da zama a kujerar shugaban PDP, za su tattara su koma wasu jam'iyyun
  • Amma a cewar Mista Eze, ya kamata Damagum ya yi abin da ya dace kada ya ƙarisa zubar da mutuncinsa a siyasa

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jigon jam'iyyar APC, Eze Chukwuemeka Eze, ya yi kira ga fusatattun ƴan majalisar tarayya 60 na PDP da su sauya tunani, ka da su sauya sheƙa daga jam'iyyarsu.

Idan baku manta ba Legit Hausa ta kawo muku rahoton cewa mambobin majalisar wakilan tarayya 60 sun yi barazanar ficewa daga jam'iyyar PDP.

Kara karanta wannan

Tsohon mataimakin shugaban majalisa ya sauya sheƙa daga jam'iyyar PDP zuwa APC

Atiku, Bala Muhammed da Gwamna Makinde.
Jigon APC ya bai wa yan majalisar PDP 60 shawara kada su sauya sheka Hoto: OfficialPDPNig
Asali: Facebook

Ƴan majalisar sun buƙaci muƙaddashin shugaban PDP na ƙasa, Umar Iliya Damagum, ya yi murabus ko kuma sun sauya sheƙa zuwa wasu jam'iyyun, Premium Times ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

PDP: Eze ya roki ƴan majalisar

Sai dai da yake martani kan haka, jigon APC Mista Eze ya buƙaci dukkan masu kishin ƙasa su taimakawa ƴan majalisar su tsaya a PDP.

Mista Eze ya bayyana haka ne a wata sanarwa da aka rabawa manema labarai a Patakwal, babban birnin jihar Ribas, kamar yadda Leadership ta tattaro.

Jigon jam’iyyar APC ya ce ‘yan majalisar dokokin jam’iyyar adawa, sun cancanci yabo saboda yunƙurin da suka yi na kubutar da jam’iyyar daga ƴan zagon ƙasa.

Ya zargi Damagum da hada baki da jiga-jigan makiyan PDP da gangan don gurgunta kokarin da ake yi na tabbatar da shugabanci a dukkan matakan jam'iyyar.

Kara karanta wannan

Kano: 'Yaran' Kwankwaso sun shiga gagarumar matsala kan dakatar da Ganduje

Eze ya nuna mamakinsa kan yadda muƙaddashin shugaban PDP ya bari mutuncinsa ya zube da kuma shiga cikin waɗanda ke ƙulla makirci lalata tsagin adawa.

Dangane da zargin cin hancin $30,000 da ministan Abuja ya ɗora wa shugabannin PDP, babban ɗan siyasar ya buƙaci hukumomin da abun ya shafa su gudanar da bincike mai zurfi.

Yadda Tinubu zai sasanta rikicin Kano

Kuna da labarin cewa tsohon mataimakin shugaban APC ya buƙaci Bola Tinubu ya sulhunta Kwankwaso da Ganduje domin warware rikicin siyasar Kano.

Salihu Lukman ya ce wannan dama ce ga Tinubu da manyan jiga-jigan APC da za su jawo Kwankwaso kuma su ceto siyasar Ganduje.

Asali: Legit.ng

Online view pixel