Rikicin PDP: 'Yan Majalisa Sun Samo Hanyar Warware Dambarwar da Ta Dabaibaye Jam'iyya
- Ƙungiyar ƴan majalisar jam'iyyyar PDP na majalisar wakilai ta yi magana kan rikicin da ya dabaibaye jam'iyyar
- Ƙungiyar ta yi kira ga fusatattun ƴaƴan jam'iyyar da su janye dukkanin ƙararrakin da suka shigar a gaban kotu
- Kiran dai na zuwa ne yayin da ake shirye-shiryen gudanar da babban taron kwamitin majalisar zartarwa ta ƙasa na jam'iyyar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Ƙungiyar ƴan majalisar jam’iyyar PDP a majalisar wakilai a ranar Talata, 16 ga watan Afrilu, sun samo mafita kan hanyar warware rikicin da ya dabaibaye jam'iyyar.
Ƙungiyar ta buƙaci dukkanin ƙusoshin jam’iyyar da sauran masu ruwa da tsaki da su gaggauta janye duk wasu ƙararrakin da ke gaban kotu, waɗanda suka hana jam’iyyar samar da sahihin shugaba na ƙasa, cewar rahoton jaridar The Nation.
Ƙungiyar ta kuma ba gwamnatin tarayya wa'adin watanni uku na ɗaukar matakan magance matsalar rashin tsaro da ake fama da ita a ƙasar nan.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sai dai, ta ce za ta zaburar da ƴan Najeriya su tashi su kare kansu idan har ba a yi wani abu domin magance lamarin ba, rahoton jaridar The Guardian ya tabbatar.
Wace hanya za a magance rikicin PDP?
Shugaban marasa rinjaye na majalisar wakilai, Kingsley Chinda, shi ne ya bayyana hakan bayan kammala taron ƙungiyar a ranar Talata, 16 ga watan Afirilun 2024.
"Mun kammala taro na uku na ƙungiyar ƴan majalisun PDP a majalisa ta 10, kuma mun cimma matsayar gayawa duniya cewa kan mu a haɗe yake kuma a shirye muke domin gudanar da ayyukanmu a madadin ƴan Najeriya."
"Ƙungiyar ta amince da yin kira ga jiga-jigan jam'iyya, ƴan kwamitin amintattu, kwamitin zartaswa na ƙasa da kwamitin gudanarwa na ƙasa da su bi hanyoyin neman sulhu domin warware ƙararrakin da suka hana jam'iyyar samun shugaba mai cikakken iko."
- Kingsley Chinda
Shugabannin APC da PDP na cikin matsala
A wani labarin kuma, kun ji cewa kujerun shugabannin manyan jam'iyyun siyasa biyu a Najeriya na fuskantar barazana.
Shugabannin jam'iyyar APC da PDP a lokaci guda sun fuskanci kalubale daga mambobinsu game da wasu zarge-zarge.
Asali: Legit.ng