Matawalle Ya Dauki Zafi Kan 'Yan Arewa, Ya Kalubalanci Wadanda Tinubu Ya Ba Mukami
- Yayin da kungiyar Dattawan Arewa ta caccakar gwamnatin Bola Tinubu, Bello Matawalle ya yi martani kan lamarin
- Karamin ministan tsaron ya ce dole dukkan masu mukamai a gwamnatin Tinubu su fito su kare shugaban a wannan lokaci
- Wannan na zuwa ne bayan kungiyar ta yi kaca-kaca da Tinubu inda ta ce 'yan Arewa sun yi dana sanin zabensa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Karamin ministan tsaro, Bello Matawalle ya kalubalanci dukkan wadanda Shugaba Bola Tinubu ya naɗa mukami a Arewa.
Matawalle ya ce ya kamata dukkansu su fito su kare shugaban yayin da ya ke fuskantar kushewa da suka.
Wani martani Matawalle ya yi kan Tinubu?
Ministan ya na magana ne musamman ga Hakeem Baba-Ahmed wanda hadimi ne a ofishin mataimakin shugaban kasa, cewar Daily Trust.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya bukace shi da sauran wadanda ke riƙe da mukamai da su bayyanawa duniya matsayarsu kan shugabancin Tinubu.
Wannan na zuwa ne bayan martanin da Baba-Ahmed wanda shi ne kakakin kungiyar Dattawa Arewa kan Gwamnatin Tarayya.
A shafinsa na Facebook, Baba-Ahmed ya ce zai fi kyau ga gwamnatin Bola Tinubu idan har Matawalle ya lissafo ayyukan da ya yi a matsayinsa na minista.
Baba-Ahmed ya yi martanin ne bayan Matawalle ya caccaki kungiyar da rashin amfani a Arewa.
Matawalle ya ce ya na mamakin yadda wadanda ke riƙe da mukamai a Arewa suka yi shiru yayin da ake caccakar gwamnatin Bola Tinubu.
Matawalle ya basu shawara game da Tinubu
"Ya kamata duk wani mai mukami a gwamnatin Tinubu ciki har da Baba-Ahmed ya fito ya kare muradun wannan gwamnati."
"Dukkan 'yan Arewa da ke wannan gwamnati, dole mu fitar da matsaya daya da kuma goyon bayan gwamnati domin samun nasararta."
"Wannan ba lokacin shiru ba ne yayin da ake barazana da farfaganda ga gwamnatin Tinubu, dole mu kare ta ko kuma mu fita a gwamnatin."
- Bello Matawalle
Tinubu ya dauki mataki kan tsaron Zamfara
Kun ji cewa Shugaba Bola Tinubu ya yi alkawarin kawo karshen matsalar tsaro da ta addabi jihar Zamfara da sauran wurare.
Tinubu musamman ya yi magana da Gwamna Dauda Lawal inda ya bashi tabbacin kawo karshen matsalar.
Asali: Legit.ng