Dalilin da Ya Sa Muka Gayyaci Nasir El-Rufai Zuwa Borno Inji Gwamnatin Zulum
- Gwamnatin jihar Borno ta tabbatar da gayyatar tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai
- Mai bawa gwamnan shawara ce, Fatima Muhammad Abbas, ta bayyana dalilan gayyatar tsohon gwamnan Kadunan a shafinta na X.
- A wurin taron, Malam Nasir El-Rufai ya yi wasu jawabai masu kama da martani wa magajinsa, Sanata Uba Sani.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Ziyarar da tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru El-Rufai ya kai jihar Borno ta jawo ka-ce-na-ce.
Hakan ya biyo bayan ziyarce-ziyarcen da ya kai ne ga wasu 'yan jam'iyyar adawa wanda har hakan ya kai ga hasashen cewa yana shirin chanja sheƙa.
Amma a na ta bangaren, gwamnatin jihar Borno ta bayyana dalilai da suka sa ta gayyaci tsohon gwamnan jihar Kadunan, wanda ta bayyana cewa ziyarar bata da alaka da siyasa
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Dalilin gayyatar El-Rufai Borno
Mai bawa gwamnan shawara ce, Fatima Muhammad Abbas, ta bayyana dalilan a shafinta na X.
Ta bayyana cewa gwamnatin ne da kanta ta gayyace shi domin ya gabatar da takarda a wurin horo na musamman.
Gwamnatin Babagana Umara Zulum ta yi wa ma'aikata horo ne a kan kwarewa wurin zartar da aikace-aikacen gwamnati.
El-Rufai ya yi martani wa Uba Sani
A kwanakin baya dai gwamna Uba Sani ya zargi El-Rufai da barin tarin bashi a jihar Kaduna, wanda hakan ke kokarin hana ayyukan raya kasa a fadin jihar.
Tsohon gwamnan jihar Kadunan ya yi wani zance mai kama da martani wa magajin nasa, Uba Sani, a wurin taron. Ga abinda ya ce kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito:
"Ba na son zama ubangida, shi ya sa ba na tsoma baki a cikin abin da ke faruwa a Kaduna, ina son shi (gwamnan) ya koyi aikin da kansa."
"Ya kamata shugaba ya samu mutanen kirki da za suyi aiki tare. Allah ne kadai zai iya yin komai shi kadai, komai nagartar ka a matsayinka na shugaba, za ka zama ne kamar mutanen da ke kusa da kai, shi ya sa ake cewa gwargwadon nagartar ma'aikatan gwamnatinku, gwargwadon yadda za ku cigaba.”
- Nasir El-Rufai
El-Rufai ya ziyarci sanatan PDP
A wani rahoton kuma, kun ji cewa tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, ya kai ziyara gidan Sanata Abdul Ningi, wanda majalisar dattawa ta dakatar kwanan nan.
Majalisa ta dakatar da Sanata Ningi, mamban jam'iyyar PDP mai wakiltar Bauchi ta Tsakiya saboda zargin cushe a kasafin kuɗin 2024
Asali: Legit.ng