Gwamna Ya Naɗa Matashi Ɗan Shekara 37 a Matsayin Sabon Mataimakin Gwamna

Gwamna Ya Naɗa Matashi Ɗan Shekara 37 a Matsayin Sabon Mataimakin Gwamna

  • Gwamna Obaseki na jihar Edo ya ɗauki sabon mataimakin gwamna jim kaɗan bayan majalisar dokoki ta tsige Kwamred Philip Shaibu
  • Bayanai sun nuna cewa shirye-shirye sun yi nisa wajen rantsar da Marvellous Omobayo Godwin a gidan gwamnati da ke Benin ranar Litinin
  • Sabon mataimakin gwamnan ɗan shekara 37 a duniya ya yi takara karƙashin inuwar jam'iyyar Labour Party a zaɓen 2023

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Edo - Gwamna Godwin Obaseki na jihar Edo ya zaɓi Marvellous Omobayo Godwin, a matsayin sabon mataimakin gwamna.

Wannan na zuwa ne sa'o'i ƙalilan bayan majalisar dokokin jihar ta tsige tsohon mataimakin gwamna, Kwamared Philip Shaibu.

Gwamna Godwin Obaseki.
Dan shekara 39 ya zama sabon mataimakin gwamnan Edo Hoto: @GovernorObaseki
Asali: Twitter

Majalisar ta ɗauki wannan matakin ne bayan karɓar rahoton kwamitin da ya gudanar da bincike kan laifuffukan da ake zargin Shaibu ya aikata.

Kara karanta wannan

Emefiele: Kotu ta ɗauki mataki 1 kan tsohon gwamnan CBN bayan EFCC ta ƙara gurfanar da shi

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kamar yadda Channels tv ta tattaro, za a rantsar da Omobayo ranar Litinin, 8 ga watan Afrilu, 2024 a fadar gwamnatin jihar Edo da ke Benin City.

Rahotanni sun bayyana cewa abokai da masu fatan alheri sun hallara a wurin bikin rantsarwar domin shaida fara aikin sabon mataimakin gwamna.

Jaridar Daily Trust ta tabbatar da naɗa sabon mataimakin gwamnan a rahoton da ta tattaro yau Litinin.

Taƙaitaccen bayani kan Omobayo Godwin

An haifi Omabayo ranar 19 ga watan Yuli, 1986 a yankin ƙaramar hukumar Akoko-Edo a jihar.

Ɗan kimanin shekaru 37 a duniya ya kammala karatun digiri na farko a ɓangaren ilimin injiniya kana ya yi digiri na biyu a fannin shugabanci a jami'ar Benin (UNIBEN).

Ya kasance cikakken mamba a kungiyar Injiniyoyi ta Najeriya (NSE) da kuma ƙungiyar COREN ta ƙasa.

Kara karanta wannan

Majalisa ta tsige mataimakin gwamnan PDP, bayanai sun fito

Kafin sabon nadin da aka yi masa, ya yi aiki a matsayin babban Injiniya a kafanin 'Dresser Wayne West Africa Limited' inda ya ya nuna gogewarsa a yankin Kudu maso Kudu.

An kuma gano cewa sabon mataimakain gwamnan ya shiga harkokin siyasa tsundum a yankin ƙaramar hukumarsa.

Bugu da ƙari, shi ne ɗan takarar kujerar mamban majalisar wakilan tarayya a mazaɓar Akoko-Edo karkashin inuwar Labour Party (LP) a zaɓen 2023.

Yadda majalisa ta tsige Shaibu

A wani rahoton na daban majalisar dokokin jihar Edo ta ɗauki matakin tsige mataimakin gwamnan jihar, Philip Shaibu, daga kan muƙaminsa.

Ƴan majalisar sun ɗauki wannan matakin ne biyo bayan gabatar da rahoton kwamitin bincike kan zarge-zargen da ake yi wa Shaibu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel