Jerin Jajirtattun Mata 4 da Ke Rike da Kujerun Majalisar Dattawa Yau a Siyasa
Abuja - A zaben 2023, an samu wasu ‘yan siyasa mata da suka lashe zaben majalisar dattawa a Najeriya, suka doke maza a takara.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.
Rahotonmu ya kawo jerin matan da ake damawa da su a majalisa da irin ayyukansu.
Matan da ke Majalisar dattawa
1. Ireti Heebah Kingibe (Abuja, LP)
Sau uku Ireti Heebah Kingibe ta na neman kujerar sanatar birnin tarayya Abuja, amma sai a zaben 2023 ta yi nasarar doke Phillip Aduda.
Sanatar ta sha alwashin amfani da albashita wajen taimakawa mutanen karkara a Abuja, yanzu ita ce shugabar kwamitin mata a majalisar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tun 1990s ta shiga siyasar jam’iyyar SDP yanzu tana kokarin inganta ilmi a Abuja. 'Yaruwar ta ce ta auri Janar Muratala Mohammad.
2. Ipalibo Harry Banigo (Ribas, PDP)
A yau Ipalibo Harry Banigo tana wakiltar mazabar Yammacin Ribas a majalisa bayan ta yi mataimakiyar gwamna a mulkin Nyesom Wike.
Kafin zuwanta majalisar dattawa, likitar ta rike mukamai da yawa a gwamnatin Ribas. A yanzu ta na shugabantar kwamitin kiwon lafiya.
Banigo ta canji wata macen Betty Apiafi a kujerar sanata a PDP. ‘Yar siyasar tana cikin sanatocin adawa da ke fadawa gwamnati gaskiya.
3. Idiat Oluranti Adebule (Legas, APC)
Kamar Sanatar Ribas ta yamma, Ita ma Idiat Oluranti Adebule ta taba zama mataimakiyar gwamnar Legas lokacin Akinwumi Ambode.
Kwanan nan Sanatar ta rabawa mutane kusan 10, 000 kayan abinci da aka shiga matsi, kwanakin baya ta taba raki domin manoma.
Daga baya Sanata Godswill Akpabio ya nada Idiat Oluranti Adebule a matsayin shugabar kwamitin yaki da talauci da kula da walwala.
4. Natasha Akpoti-Uduaghan (Kogi, PDP)
Natasha Akpoti-Uduaghan ta shigo majalisa a 2023 bayan nasara a shari’ar zaben 2023 a karkashin jam'iyyar hamayya ta PDP.
‘Yar siyasar ta yi nasara a kan ‘dan majalisar APC mai rinjaye ta karbe kujerar Sanata domin wakiltar mutanen yankin Kogi ta tsakiya.
Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan ta tashi tsaye wajen taimakon mutanenta. ‘Yar siyasar shekarar ta na cikin shugaban kwamitoci a yau.
FIRS ta samu N12.3tr a 2023
Kuna da labari cewa Hukumar FIRS ta ce ta samu kudin shigar da ba a taba gani a tarihin Najeriya ta babin kudin shiga a shekarar bara.
A shekarar 2023, Zacch Adedeji ya ce gwamnatin tarayya ta samu Naira tiriliyan 12.3 ta haraji a lokacin da aka shiga cikin matsin tattali.
Asali: Legit.ng