Watanni 2 da Maganar Komawa APC, Abba Ya Dauko Binciken Ganduje da Iyalinsa a Kano
- Yanzu an daina maganar cewa Abba Kabir Yusuf da ‘Yan Kwankwasiyya za su sauya-sheka daga jam’iyyar NNPP
- Akasin haka, said ai aka ji gwamnatin Kano ta dage sai an binciki Abdullahi Umar Ganduje da wasu na kusa da shi
- Tsohon gwamnan ya ce tuggu kurum aka shirya masa, Gwamnatin Abba ta fake da cewa an taba dukiyar al’umma
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.
Kano - Kwanakin baya aka yi ta tunanin babu mamaki Abba Kabir Yusuf ya amsa tayin Abdullahi Umar Ganduje na komawa APC.
Yanzu kuma sai aka ji gwamnatin Kano ta dawo da karfinta wajen binciken tsohon gwamnan Kano kuma shugaban APC na kasa.
Daily Trust ta ce gwamnatin Abba Yusuf ta fara da shigar da kara kan Abdullahi Ganduje, mai dakinsa Dr. Hafsah da yaronsa Abba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ana tuhumar wadannan mutane da zargin karbar rashawa da karkatar da dukiyar gwamnati a lokacin da Ganduje yake ofis a Kano.
Bayan shari’ar zaben gwamnan Kano a kotun koli, an yi tunanin bangarorin biyu sun yi sulhu domin NNPP ta cigaba da mulkin jihar.
Kafin alkalai suyi hukunci a kotun koli, Abba Kabir ya rasa kujerarsa ga Nasiru Gawuna, hakan ya sa APC ta zo daf da karbe mulki.
Yanzu sanarwa ta fito daga gwamnatin Kano, an kakkabe takardu, an kafa kwamiti da zai binciki Dr. Ganduje da aikin gwamnatinsa.
Abba ya binciki Ganduje ko kuwa?
Wasu suna ganin ya kamata a binciki zargin da ke kan wuyan gwamnatin da ta wuce.
Amma kuma akwai wadanda suke ganin cewa bita-da-kulli ake yi wa Ganduje saboda sabanin siyasa, zargin da gwamna ya watsar.
Mutane irinsu Dr. Fahad Danladi sun ce sun ji dadin wannan batu domin barnar da aka yi a gwamnatin baya ta cancanci a yi bincike.
Dambarwar Gwamna Abba da Sarkin Kano
Tun jiya ake yada labari cewa Abba Kabir Yusuf ya ce shi da Sarkin Kano tamkar Hasan da Husaini ne, mun kawo rahoto a kan batun.
Akwai magana a kan masaratun Kano amma babu inda Gwamnan Kano ya yi zancen a ranar hawan Nasarawa, Abba bai fadi haka ba.
Asali: Legit.ng