Jigon APC Ya Fadi Abin da Zai Hana Tinubu Yin Shekara 8 Kan Karagar Mulki
- Yekini Nabena na da ra'ayin cewa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu sai ya yi shekara takwas kan karagar mulkin Najeriya
- Tsohon mataimakin sakataren yaɗa labaran na jam'iyyar APC ya yi nuni da cewa duk wasu ƙulle-ƙullen da ƴan adawa suke yi ba zai yi tasiri ba
- Ya bayyana cewa mutanen yankin Kudancin Najeriya yanzu sun dawo cikin hayyacinsu sun daina faɗa da juna domin wani yankin ya amfana
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Tsohon mataimakin sakataren yaɗa labarai na jam’iyyar APC, Yekini Nabena, ya ce Shugaba Bola Tinubu sai ya yi shekara takwas a kan mulki.
Yekini ya bayyana cewa batun haɗaka da shirin da ƴan adawa suke na amfani da halin ƙuncin da ake ciki a ƙasa, domin Tinubu ya kasa yin wa'adi biyu a ofis ba zai yi tasiri ba, cewar rahoton jaridar The Punch.
Kalaman nasa na zuwa ne a daidai lokacin da ake tattaunawa kan hadakar jam’iyyun adawa domin samar da babbar jam'iyya wacce za ta kawar da Tinubu a zaɓen 2027.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jigon na APC ya kuma bayyana cewa babu wani juyin mulkin siyasa a majalisar dattawa da zai sanya a tsige shugaban majalisar, Sanata Godswill Akpabio.
Mai jigon APC ya ce kan makomar Tinubu?
Jaridar Leadership ta ce a cikin wata sanarwa da ya fitar a Abuja ranar Talata, Nabena ya jaddada cewa bai kamata a yi wasa da haɗin kan Najeriya ba,.
A kalamansa:
"Dole ne mu gayawa masu shirin kafa babbar jam'iyya da masu shirin yin haɗaka cewa ba mu tsoro. Idan har tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari zai kammala shekarunsa takwas, Insha Allah Tinubu shi ma zai yi hakan.
"Babu batun wata babbar jam'iyya ko haɗaka da zai taka masa burki. Yankin Kudu ba za su sake faɗa da juna ba domin wani yankin ya amfana. Lokacin rarrabuwar kai a Kudancin Najeriya ya wuce.
"Ina fatan cewa ko kafin zaɓe mai zuwa, sakamakon sauye-sauyen da ake yi a yanzu zai sanya masu tunanin kafa wata babbar jam'iyya su kasance ba su da wani zaɓi face su yarda da rashin nasara kafin zaɓen."
Batun dakatar da shugabar matan APC
A wani labarin kuma, kun ji cewa shugabar matan jam'iyyar APC da aka ɗakatar a jihar Kaduna, Maryam Suleiman, ta yi bayyana cewa ba ta yi nadamar sukar Gwamna Uba Sani ba.
Maryam ta haƙiƙance cewa tana na kan bakanta kan sukar gwamnan bisa abin da ta kira cin amanar Nasir El-Rufa'i da ya yi.
Asali: Legit.ng