Shugaba Tinubu Zai Sake Fita Daga Najeriya Zuwa Ƙasar Waje a Watan Azumi, Bayanai Sun Fito

Shugaba Tinubu Zai Sake Fita Daga Najeriya Zuwa Ƙasar Waje a Watan Azumi, Bayanai Sun Fito

  • Bola Ahmed Tinubu zai shilla zuwa Dakar, babban birnin ƙasar Senegal domin halartar bikin rantsar da zababben shugaban ƙasa
  • A wata sanarwa da fadar shugaban ƙasa ta fitar, Tinubu zai yi wannan tafiya zuwa Senegal kuma ya dawo gida Najeriya a ranar 2 ga watan Afrilu
  • Tinubu, wanda ke jagorantar ƙungiyar ECOWAS, zai bi sahun takwarorinsa na yammacin Afirka zuwa wajen shaida rantsuwar Bassirou Diomaye Faye

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya shirya barin birnin Abuja zuwa Dakar, babban birnin ƙasar Senegal ranar Talata, 2 ga watan Afrilu, 2024.

Shugaba Tinubu zai tafi ƙasar Senegal ne domin halartar bikin rantsar da zaɓaɓɓen shugaban ƙasar, Bassirou Diomaye Faye gobe Talata.

Kara karanta wannan

Abin da Bola Tinubu ya faɗawa manyan Malamai da Sarakuna a wurin buɗa baki a Aso Villa

Bola Ahmed Tinubu.
Tinubu zai halarci rantsar da sabon shugaban Senegal Hoto: Bayo Onanuga
Asali: Twitter

Hakan na ƙunshe ne a wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban ƙasa, Ajuri Ngelale ya fitar ranar Litinin, 1 ga watan Afrilu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce Shugaba Tinubu, wanda zai halarci bikin bisa gayyatar da ƙasar ta aiko masa, zai dawo gida Najeriya jim kaɗan bayan kammala rantsar da shugaban ƙasar.

Yadda Faye ya zama shugaban Senegal

Bassirou Diomaye Faye, ɗan shekara 44 a duniya, wanda ya lashe zaɓen shugaban ƙasar Senegal, ya zama shugaban ƙasa mafi ƙarancin shekaru a nahiyar Afirka.

A wani rahoto da BBC ta fitar a baya, an sake shi ne makonni kadan kafin zaben bayan ya shafe watanni a gidan yari kuma ya samu nasarar lashe zaben.

Zababben shugaban kasar da ke shirin zama shugaba mafi karancin shekaru a Senegal bayan rantsar da shi, zai iya girgiza fagen siyasa tare da kawo manufofin sauyi a kasar.

Kara karanta wannan

Bola Tinubu ya ɗauko ɗan Arewa, ya naɗa shi a babban muƙami a watan azumi

A ranar rantsarwan, ana sa ran Bola Tinubu zai bi sahun takwarorinsa na ƙasashen Yammacin Afirka a Dakar, babban birnin Senegal.

Sanarwar ta ce:

"Shugaban kasar zai yi wannan tafiya tare da rakiyar ministan harkokin kasashen waje, Ambasada Yusuf Maitama Tuggar da wasu manyan jami'an gwamnati."

Fedrick Nwabufo, babban mai taimakawa shugaban ƙasa kan harkokin hulɗa da jama'a ne ya wallafa sanarwar a shafinsa na manhajar X.

Abubuwa 10 game da Tinubu

A wani rahoton Shugaba Bola Ahmed Tinubu , GCFR, shugaban Najeriya na yanzu, ya yi bikin cika shekaru 72 da haihuwa a ranar Jumu'a, 29 ga Maris, 2024.

Legit Hausa ta tattaro muku abubuwa 10 da ya kamata ku sani game da Shugaba Tinubu wanda ƙe shirin cika shekara ɗaya a kan madafun iko.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262