Rikicin El-Rufai da Uba Sani: Shehu Sani Ya Fadi Gaskiyar Lamari Kan Bashin Kaduna
- Sanata Shehu Sani ya bayyana yadda aka yi ci mutuncinsa bayan ya ki amincewa da karbar bashi da gwamnatin jihar ta yi a baya
- Sani ya ce daman ya san haka zai faru ganin yadda bashin zai yi tasiri musamman a irin wannan lokaci da ake ciki a jihar
- Wannan na zuwa ne bayan Gwamna Uba Sani ya yi korafi kan bashin da ya gada daga gwamnatin da ta gabata a jihar
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Kaduna – Sanata Shehu Sani ya yi martani kan matsalar bashi a jihar Kaduna da ake cece-kuce a kai.
Sani ya ce idan da tsohon gwamnan jihar, Nasir El-Rufai ya ji shawararsa da ba a shiga wannan hali da ake ciki ba, cewar Vanguard.
Abin da Sani ya ce kan bashin Kaduna
Sanatan ya bayyana haka ne yayin hira da manema labarai ya ce an ci mutuncinsa kan ba El-rufai shawara game da bashin $350m daga Bankin Duniya, cewar AIT News.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
“An ci zarafi na da cin mutunci saboda naki amincewa da bashin da ake shirin karba.”
“Kamar yadda Annabi Ludu a cikin Injila, ya gargadi mutane sauran annabawa sun gargadi mutane amma sun ki su ji.”
“Nima na gargadi mutanen jihar nan, amma suka ce bashin kudin zai kawo musu aljanna, zuma da sauran kayan dadi.”
“A yanzu, idan ka duba abin da aka fada a jihar, babu wani abin da na fada wanda bai zo ba, yanzu an shake wuyan jihar Kaduna saboda kudin da aka gagara biya.”
- Shehu Sani
Uba Sani ya yi korafi kan bashin Kaduna
Wannan na zuwa ne bayan Gwamna Uba Sani ya yi korafi kan yawan bashi da ya gada a jihar Kaduna.
Gwamna ya bayyana haka ne a ranar Asabar 30 ga watan Maris inda ya ce bashin ya na cinye kudin da suke samu daga Gwamnatin Tarayya.
Ya ce a yanzu gwamnatin jihar na biyan kusan ninki uku na bashin da tsohon gwamnan jihar, Nasir El-Rufai ya karba saboda tashin dala.
APC ta dakatar da shugabar matan jam’iyyar
Kun ji cewa, jam’iyyar APC a jihar Kaduna ta dakatar da shugabar matan jam’iyyar, Maryam Suleiman kan bashin jihar Kaduna.
Jam’iyyar na zargin Maryam da cin mutuncin Gwamna Uba Sani bayan ya yi korafi kan bashin da ake bin jihar.
Asali: Legit.ng