Jam'iyyar PDP Ta Waiwayo Kan Wike da Sauran Wadanda Suka Juyawa Atiku Baya a 2023

Jam'iyyar PDP Ta Waiwayo Kan Wike da Sauran Wadanda Suka Juyawa Atiku Baya a 2023

  • Ƴa ƴan jam'iyyar PDP da suka yi wa jam’iyyarsu yankan baya a zaɓen 2023, za a hukunta su a lokacin da ya dace
  • Wannan ita ce matsayar Umar Bature, sakataren tsare-tsare na ƙasa na PDP a yayin taron kwamitin gudanarwa na jam'iyyar na ƙasa a ranar Talata, 26 ga watan Maris
  • Bature ya buƙaci shugabannin jam’iyyar na jihohi da su miƙa sunayen mambobinsu da suka yi zagon ƙasa domin ɗaukar matakin da ya dace

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Jam’iyyar PDP ta jaddada matsayin ta na hukunta wasu mambobinta da suka ci dunduniyarta a babban zaɓen 2023.

Kyaftin Umar Bature (mai ritaya), sakataren tsare-tsare na ƙasa na jam’iyyar PDP, ya bayyana hakan.

Kara karanta wannan

Jam'iyyar NNPP ta samu sabon shugaba na kasa, cikakkun bayanai sun fito

PDP za ta yi hukunci
Jam'iyyar PDP ta shirya hukunta wadanda suka yi mata zagon kasa a zaben 2023 Hoto: Official Peoples Democratic Party (PDP)
Asali: Facebook

Ya bayyana hakan ne a yayin wani taron kwamitin gudanarwa na jam’iyyar na ƙasa (NWC), da shugabannin jam’iyyar na jihohi 36 a Abuja, a ranar Talata, 26 ga watan Maris 2024.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A yayin taron NWC da aka yi a ranar Talata, Bature ya buƙaci shugabannin jam’iyyar na jihohi da sauran masu ruwa da tsaki da su tona asirin waɗanda ke da hannu domin ɗaukar matakin da ya dace a kansu.

Wane mataki jam'iyyar PDP za ta ɗauka?

A cewarsa, ƴaƴan jam'iyyar da dama na ta kiran a dakatar da wasu jiga-jigan jam'iyyar PDP masu hannu a zagon ƙasan.

Sai dai, ya ƙara da cewa shugabannin jam’iyyar na jihohi su ne ke da alhakin ɗaukar irin wannan matakin a jihohinsu, cewar rahoton jaridar Vanguard.

A kalamansa:

"Za ku gaya mana wanda ya ci dunduniyar jam’iyya da wanda bai yi ba, bisa ga hakan majalisar zartaswa ta ƙasa za ta yanke hukunci. Ku rubuto mana ku gaya mana abin da ya faru, koma menene ya faru.

Kara karanta wannan

Tsadar iskar gas: Jigon APC ya bukaci Shugaba Tinubu ya tausayawa talaka

"Ina kuma son shugaban riƙo na ƙasa da ya kira shugaban jam'iyya na jihar Kuros Ribas da ya gaya mana abin da yake faruwa a jihar, saboda akwai abubuwa da dama da muke ji a kafafen yaɗa labarai. Muna son mu san haƙiƙanin abin da ke faruwa."

PDP ta buƙaci Akpabio ya yi murabus

A wani labarin kuma, kun ji cewa jam’iyyar PDP ta bukaci Sanata Godswill Akpabio da ya gaggauta sauka daga kan kujerarsa ta shugaban majalisar dattawa.

PDP ta ce hakan ne kawai zai ba da damar a gudanar da bincike kan zargin cewa an yi cushen Naira tiriliyan 3.7 a cikin kasafin kudin 2024.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng