Gwamnan Arewa Ya Naɗa Mutane Sama da 250 a Muhimman Muƙamai Ana Tsaka da Azumi

Gwamnan Arewa Ya Naɗa Mutane Sama da 250 a Muhimman Muƙamai Ana Tsaka da Azumi

  • Farfesa Babagana Umaru Zulum ya naɗa sababbin hadimai 168 da mambobin majalisun gudanarwa na hukumomi 15 a jihar Borno
  • Gwamnan ya sanar da haka ne a wata sanarwa da sakataren gwamnatin Borno, Alhaji Bukar Tijjani ya fitar ranar Litinin a Maiduguri
  • Wannan na zuwa ne kwanaki bayan gwamnatin Borno ta ware N2.1bn domin biyan hakkokin ƴan fansho da ma'aikatan da suka tafi hutu

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Borno - Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umaru Zulum, ya amince da naɗin sababbin mutane 168 masu taimaka masa.

Gwamna Zulum ya kuma amince da naɗin mutum 104 a matsayin 'yan majalisar gudanarwa na hukumomin gwamnati 15 a jihar Borno.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Bola Tinubu Ta faɗi gaskiya kan biyan kuɗin fansa yayin ceto ɗaliban Kaduna

Gwamna Zulum.
Babagana Zulum ya yi sababbin naɗe-naɗe a Borno Hoto: Prof. Babagana Umara Zulum
Asali: Twitter

Hakan na ƙunshe ne a wata sanarwa da sakataren gwamnatin Borno, Alhaji Bukar Tijjani, ya fitar ranar Litinin a Maiduguri, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Zulum: An jero muƙaman da aka naɗa

Ya ce wadanda aka nada sun hada da manyan mataimaka na fasaha (STA) 9, manyan mataimaka na musamman (SSAs) 81 da mataimaka na musamman (SAs) 78.

SSG ya kuma lissafa wasu mutum 104 da Zulum ya naɗa a matsayin shugabanni da 'yan majalisar gudanarwa na hukumomi da ma'aikatun gwamnati 15.

Sakataren ya ƙara da cewa Gwamna Zulum ya yi wannan naɗe-naɗe ne duba da ƙarfin ikon da yake da shi a tanadin sashe 208(2)d na kundin tsarin mulkin Najeriya 1999.

"Gwamnan ya taya ɗaukacin wadanda aka nada murna tare da fatan za su bayar da gudunmawar da zata kawo ci gaba a jihar Borno,"

Kara karanta wannan

Mataimakin gwamnan PDP na dab da rasa kujerarsa yayin da CJ ya kafa kwamitin mutum 7

- Sakataren gwamnatin Borno

Wasu ayyukan Zulum a Borno

Wannan naɗe-naɗe na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan Gwamna Zulum ya ba da umarnin fitar da N2.1bn domin biyan ma'aikata da ƴan fansho haƙƙokinsu.

Shugaban ma’aikatan jihar Borno, Mallam Fannami ne ya bayyana haka ranar Alhamis a Maiduguri, kamar yadda Daily Nigerian ta ruwaito.

Bugu da ƙari, gwamnatin Borno ta fara rabon hatsi ga gidaje 100,000 a Maiduguri da kewaye domin rage radadin matsin tattalin arziki.

Kano: Gwamna Abba ya musanta kashe N6bn

A wani rahoton na daban Gwamnan jihar Kano Abba Yusuf ya musanta rahotannin da aka yada cewa gwamnatinsa ta ware Naira biliyan 6 don ciyar da mutane a Ramadana.

Idan ba ku manta ba, ganin yawan kudin da aka ce Abba ya ware ya sa APC ta fara zargin lauje cikin nadi a harkar ciyarwar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262