Gwamnan APC Ya Gana da Tinubu Kan Muhimmin Batu da Ya Shafi Tsaro a Jihar Arewa
- Gwamna Ahmed Ododo na jihar Kogi ya ziyarci shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu kan batun tsaro ranar Laraba da ta gabata
- A wata sanarwa da kakakin gwamnan ya fitar, ya ce Ododo ya yi wa Tinubu bayanin halin da ake ciki a jihar Kogi
- Shugaba Tinubu ya jinjinawa gwamnan bisa yadda ya fara mulki da ƙafar dama, inda ya tabbatar masa da cewa zai mara masa baya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
FCT, Abuja - Gwamnan jihar Kogi, Ahmed Ododo ya kai ziyara ta musamman ga Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu a fadar gwamnati da ke birnin tarayya Abuja.
Yayin wannan ziyara, Gwamna Ododo ya tattauna da Shugaba Tinubu kan sha'anin tsaro a jihar Kogi da ke Arewa ta Tsakiya a Najeriya.
Wannan na kunshe ne a wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Ismaila Isah, ya fitar, kamar yadda Channels tv ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Abin da Ododo ya faɗawa Tinubu
Ya ce gwamnan ya faɗawa shugaba Tinubu halin da ake ciki game da tsaro a jihar Kogi, gami da kokarin da gwamnatinsa ke yi na inganta tsare-tsaren samar da tsaro mai ɗorewa.
Gwamnan ya kuma yabawa shugaba Tinubu kan kokarinsa na ganin an gaggauta daukar matakin magance kalubalen ƙarancin abinci a kasar nan.
Sannan ya sanar da shugaban kasar irin kalaman yabon da suka fito daga al'ummar jihar Kogi biyo bayan rabon tallafin kayan abinci a jihar a watan jiya.
Gwamna Ododo ya kuma tabbatar da kudirinsa na samar da abinci a jihar Kogi ta hanyar tsaftace gonaki da tallafawa manoma domin bunƙasa harkokin noma da sarrafa kayan abinci.
Ya kuma yabawa shugaba Tinubu kan hanzari da jajircewar ma’aikatar ayyuka ta ƙasa wajen ganin an kammala ayyukan titunan gwamnatin tarayya a kan lokaci a jihar Kogi.
Tinubu ya jinjinawa sabon gwamnan
A nasa jawabin, shugaba Tinubu ya yabawa Gwamna Ododo bisa yadda ya fara taka rawar gani a matsayin gwamnan jihar Kogi, kamar yadda Tribune ta rahoto.
Ya kuma ba shi tabbacin cewa gwamnatin tarayya karkashin jagorancinsa za ta ci gaba da mara masa baya a kokarinsa na kawo sauyi a jihar.
Gwamna Radɗa ya tallafawa mata a Katsina
A wani rahoton kuma Malam Dikko Radda ya rabawa mata da ƴan matan da hare-haren bindiga ya shafa tallafin N150,000 domin su fara sana'a.
Gwamnan Katsina ya kuma raba tallafin N100,000 ga iyaye mata da ƴan matan da cutar korona ta durkusar da kasuwancinsu a kananan hukumomi 34 na Katsina.
Asali: Legit.ng