Mataimakin Gwamna Ya Gamu da Babbar Matsala 1 Yayin da Majalisa Ke Shirin Tsige Shi
- Mataimakin gwamnan jihar Edo ya yi rashin nasara a babbar kotun tarayya yayin da yake kokarin hana majalisar dokoki tsige shi
- Alkalin kotun, mai shari'a James Omotoso, ya ƙi aminta da ko ɗaya daga cikin buƙatun Kwamared Philip Shaibu
- Tun da farko, Shaibu ya roki kotun ta yi hukuncin wucin gadi na dakatar da waɗanda ake ƙara daga bin matakan sauke shi daga kujerar mataimakin gwamna
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Babbar kotun tarayya mai zama a Abuja ta ƙi amincewa da buƙatar mataimakin gwamnan jihar Edo, Kwamared Phiip Shaibu.
Mai shari'a James Omotoso ya yi fatali da buƙatar Shaibu na dakatar da majalisar dokokin jihar Edo daga yunƙurin tsige mataimakin gwamnan, Channels tv ta ruwaito.
Wane buƙatu Shaibu ya gabatar gaban kotu?
A karar da ya shigar, Shaibu ya roƙi kotun ta bada umarnin cikin shari'a da zai dakatar da waɗanda yake ƙara daga na uku zuwa na biyar daga ci gaba shirin tsige shi, a cewar rahoton Daily Post.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Mataimakin gwamnan ya buƙaci alkalin ya hana waɗanda yake ƙara kafa kwamitin da zai bincike zarge-zargen da ake masa har sai an yanke hukuncin karshe a karar.
Ya nemi hukuncin wucin gadi na hana wadanda ake tuhuma, su kansu ko wakilansu, ɗaukar kowane mataki da nufin tsige shi daga mukamin mataimakin gwamnan jihar Edo.
Kotu ta yanke hukunci
Amma a hukuncin da kotu ta yanke ranar 13 ga watan Maris, wanda labarin ya fito ranar Litinin, mai shari’a James Omotosho, ya ki amincewa da buƙatun mataimakin gwamnan.
"Ba mu amince da buƙatar hukuncin wucin gadin da aka shigar ranar 8 ga watan Maris, 2024 ba"
in ji alkalin.
A halin da ake ciki kuma, a zaman kotu na ranar Talata, alkali ya sanya ranar Laraba don sauraron wata buƙatar da mai shigar da kara, Shaibu, ya sake gabatarwa.
Wannan dai na zuwa ne yayin da majalisar dokokin jihar Edo ta umarci babban alkalin jihar ya kafa kwamitin da zai bincike zarge-zargen da ake yi wa mataimakin gwaamna.
Tinubu ya hango sabon gwamnan Edo
A wani rahoton kuma Bola Ahmed Tinubu ya yi hasashen cewa jam'iyyar APC za ta lashe zaben gwamnan jihar Edo mai zuwa a watan Satumba, 2024.
Shugaban ƙasa ya kuma miƙa tutar APC ga ɗan takarar gwamna, Sanata Monday Okpebholo, da abokin gaminsa, Honorabul Dennis Idahosa.
Asali: Legit.ng