Ganduje Ya Fadi Wadanda Za Su Rika Samun Mukamai Masu Gwabi a Gwamnatin Tinubu

Ganduje Ya Fadi Wadanda Za Su Rika Samun Mukamai Masu Gwabi a Gwamnatin Tinubu

  • Shugaban jam'iyyar APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje, ya yi nuni da cewa a shirye Shugaba Bola Tinubu yake ya sakawa ƴaƴan jam'iyyar
  • Ganduje ya bayyana hakan ne yayin da ya karɓi baƙuncin shugabannin jam'iyyar APC na jihohi 36 da ke ƙasar nan
  • Tun da farko dai shugabannin sun ziyarci Tinubu inda suka buƙaci ya riƙa sakawa ƴaƴan jam'iyyar da suka yi ɗawainiya da ita a zaɓen 2023

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya tabbatarwa ƴaƴan jam’iyyar APC cewa zai saka musu da muƙamai masu gwaɓi.

Shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje ne ya bayyana haka a lokacin da ya karɓi baƙuncin mambobin ƙungiyar shugabannin jam’iyyar APC na jihohi a ofishinsa da ke Abuja, cewar rahoton jaridar The Nation.

Kara karanta wannan

Rigima sabuwa: An bukaci shugaban NLC ya yi murabus, an fadi dalili

Tinubu da Ganduje
Ganduje ya kwantar da hankalin 'ya'yan jam'iyyar APC Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, Abdullahi Umar Ganduje
Asali: Facebook

A ranar Juma’a ne shugabannin jam’iyyar na jihohi 36 suka kai ziyarar nuna goyon baya ga shugaban ƙasa, Bola Tinubu, inda suka gabatar da buƙatar a riƙa sakawa ƴaƴan jam'iyyar waɗanda suka bada gudunmawa wajen samun nasarar jam’iyyar a zaɓen 2023.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tinubu zai sakawa ƴaƴan jam'iyyar APC

Da yake jawabi ga shugabannin, Ganduje ya nuna jin daɗinsa kan ziyarar da suka kai wa shugaban ƙasan, inda ya ce a shirye ya ke wajen biya musu dukkanin buƙatun da suka gabatar masa, cewar rahoton jaridar The Punch.

Da yake yaba wa shugabannin da suka kai wa shugaban ƙasa ziyarar, Ganduje ya bayyana cewa:

"Wannan wata muhimmiyar ziyara ce mai matuƙar muhimmanci da kuka kai wa shugaban ƙasa. Yayi murna da hakan. Ina so in tabbatar muku cewa ziyara irin wannan za a ci gaba da yinta.

Kara karanta wannan

Na hannun daman Atiku ya fadi nadamar da ya yi kan aiki da tsohon mataimakin shugaban kasan

"Ina kuma farin cikin sanar da ku cewa Shugaba Tinubu ya karɓi buƙatunku, musamman kan muƙaman siyasa. Yana yin wani abu a kai. Tabbas zai sakawa jajirtattun ƴaƴan jam'iyya kamar yadda ya dace.

APC na zawarcin Gwamna Mutfwang

A wani labarin kuma, kun ji cewa jam'iyyar APC ta fara zawarcin gwamnan jihar Plateau, Caleb Mutfwang, domin ya dawo cikinta.

Jam'iyyar ta ce idan har gwamnan ya na so ya samu cikar muradunsa na kawo ci gaba mai ɗorewa a jihar Plateau, sai ya sauya sheƙa zuwa APC.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng