Bayan Katobara a Zaman Makoki, Gwamnan PDP Ya Sake Shiga Matsala Kan Bukatar APC a Jihar
- Jam’iyyar APC a jihar Ribas ta bukaci Gwamna Siminalayi Fubara ya yi murabus daga kujerarsa saboda ya gaza yin katabus
- Shugaban jam’iyyar, Cif Tony Okocha shi ya shawarci gwamnan inda ya ce Fubara yana saba dokokin jihar a mulkinsa
- Sai dai gwamnatin jihar ta yi martani mai zafi inda ta ce tun bayan kafa jihar Ribas ba a taba samun gwamnan irin Fubara ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Rivers – Shugaban jam’iyyar APC a jihar Rivers, Cif Tony Okocha ya shawarci Gwamna Siminalayi Fubara ya yi murabus.
Tony Okocha ya ba Fubara shawarar ce ganin yadda ya gagara tabuka wani abun a zo a gani ga al’ummar jihar da suka zabe shi.
APC ta bukaci Fubara ya yi
Okocha ya bayyana haka ne a jiya Talata 12 ga watan Maris yayin hira da ‘yan jarisu a birnin Port Harcourt, cewar Leadership.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shugaban jam’iyyar ya zargi Fubara da saba kundin tsarin mulki Najeriya inda ya ke gudanar da gwamnati ba tare da kasafin kudi ba.
Har ila yau, Okocha ya zarge shi da kin kafa kwamitin da zai tabbatar da gudanar da zaben kananan hukumomi a jihar.
Daga cikin zarge-zargen da APC ke yi kan Fubara akwai rike kudin kananan hukumomi 23 da ke da ake ba su kowane wata.
“Gwamnan ba shi da karfin ikon rike kudin kananan hukumomi 23 a jihar wanda hakan ya sabawa dokokin kasa.”
- Tony Okocha
Martanin gwamnatin jihar Ribas
Sai dai gwamnatin jihar ta yi martani mai zafi kan wannan kira na jam’iyyar APC da ta zargi Gwamna Fubara da saba dokoki.
Kwamishinan yada labarai, Warisenibo Joe ya ce Okocha bai san ma menene ya ke faruwa ba a jihar, The Guardian ta tattaro.
Joe ya ce ba a taba samun gwamna mafi alheri a tarihin jihar Rivers ba kamar Fubara inda al’ummar jihar ke jin dadin mulkinsa.
Fubara da Akpabio sun kaure
Kun ji cewa Gwamna Siminalayi Fubara na jihar Ribas da Shugaban Majalisa, Godswill Akpabio sun yi cece-kuce a zaman makoki.
Fubara ya yi wasu maganganu kan ruguntsumin siyasa inda Akpabio ya maida masa da martani mai zafi a wajen shirin birne Herbert Wigwe.
Asali: Legit.ng