"Ka da Ka Zama Kamar Buhari": An Ba Tinubu Shawarar Magance Matsalar Rashin Tsaro

"Ka da Ka Zama Kamar Buhari": An Ba Tinubu Shawarar Magance Matsalar Rashin Tsaro

  • Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya samu muhimmin kira daga ƙungiyar Yarbawa ta Afenifere kan matsalolin da suka addabi ƙasar nan
  • Ƙungiyar ta buƙaci shugaban ƙasan da ya tashi tsaye ya nuna da gaske yake yi domin kawo ƙarshen ƴan ta'adda masu kashewa da sace mutane
  • Ta kuma yi kira ga Mai girma Tinubu da ya kawo ƙarshen halin matsin tattalin arziƙin da ƴan Najeriya suka tsinci kansu a ciki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Ƙungiyar Yarbawa ta Afenifere, a ranar Litinin, ta yi kira ga shugaban ƙasa Bola Tinubu, da ya nuna ba sani ba sabo kan ƴan ta'addan da ke addabar Najeriya.

Ƙungiyar Afenifere ta ce bai kamata shugaban ƙasan ya gaza ba kamar magabacinsa, Muhammadu Buhari, wajen magance matsalar rashin tsaro, cewar rahoton jaridar Daily Trust.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya fayyace gaskiya kan masu zargin Buhari ne ya lalata Najeriya

Afenifere ta shawarci Tinubu
Kungiyar Afenifere ta bukaci Tinubu ya kawo karshen 'yan ta'adda Hoto: @DOlusegun
Asali: Twitter

Wace shawara Afenifere ta ba Tinubu?

Ƙungiyar ta ce dole ne Tinubu ya nuna kishi da jajircewarsa wajen kawar da waɗannan mugayen mutanen masu kashewa da sace ɗarutuwan mutane.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jaridar The Punch ta kawo rahoto cewa Afenifere ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da sakataren yaɗa labaranta, Mogaji Gboyega Adejumo, da mataimakinsa, Justice Faloye suka sanya wa hannu.

Ƙungiyar ta ce zai zama babbar illa da abin takaici idan Tinubu, kamar wanda ya gabace shi, ya yi sako-sako wajen ɗaukar matakin da ya dace kan ƴan ta'addan da ke zubar da jini.

Afenifere ta kuma yi kira ga Tinubu da ya fara sake fasalin ƙasar nan domin tafiyar da gwamnatin shiyya-shiyya a ƙarƙashin tsarin Firayim Minista.

Ƙungiyar ta kuma yi kira ga shugaban ƙasan da ya tabbatar maganar da ya yi ta samar da ƴan sandan jihohi, ta tabbata.

Kara karanta wannan

A karon farko Buhari ya fadi gaskiyar yadda yake kallon salon mulkin Shugaba Tinubu

Ƙungiyar Yarbawan ta kuma koka kan halin matsin tattalin arziƙin da ake ciki a ƙasar nan, inda ta buƙaci shugaban ƙasan da ya shawo kan matsalar.

Sheikh Gumi ya ja kunnen Tinubu

A wani labarin kuma, kun ji cewa Sheikh Ahmad Abubakar Gumi, ya buƙaci shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya yi sulhu da ƴan bindiga.

Malamin addinin musuluncin ya buƙaci shugaban ƙasan da ya guji sake maimaita irin kuskuren da magabacinsa, tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya yi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng