Sanatocin Arewa Sun Yi Haramar Tsige Shugaban Majalisa Kan Badakalar N4tr a Kasafin 2024
- Masu wakiltar jihohin Arewa a majalisar dattawan kasar za su iya neman hambarar da Sanata Godswil Akpabio
- Ana zargin an yi cushen ayyukan Tiriliyoyin Nairori a kasafin kudin 2024 ba tare da sanin ‘yan majalisar tarayya ba
- Sanata Abdul Ningi ya fito fili ya jefa wannan zargi inda Sanatocin Arewa suka sa labule da Godswil Akpabio a gidansa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.
Abuja - Sanatocin Arewa a karkashin kungiyar Arewa NSG sun tunkari shugaban majalisar dattawa a kan zargin cushe a kasafin kudi.
Premium Times ta rahoto cewa ana zargin an cusa ayyuka na N4tr ta bayan fage a cikin kasafin kudin 2024 ba da sanin al’umma ba.
Sanatoci sun zauna da Akpabio a Abuja
Shugaban kungiyar SNG, Abdul Ningi (PDP, Bauchi) ya jagoranci sauran abokan aikinsa, aka tunkari Godswill Akpabio a gidansa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An yi zaman ne tare da shugabannin majalisa irinsu Barau Jibrin (APC, Kano) da Ali Ndume (APC, Borno) a gidan Akpabio a Maitama.
Akpabio ya bari an fifita Arewa a Majalisa?
Ana zargin Akpabio ya bada dama an cusa ayyuka inda aka nunawa Arewa son kai, kuma aka yi gaggawar amincewa da kundin 2024.
Jaridar ta ce ba a yi bayanin yankunan da za a aiwatar da kwangilolin ba. Tsoron Sanatocin shi ne an watsar da ayyukan Arewa.
Shugaban Majalisa da Sanatocin Arewa
Wata majiya ta ce Akpabio bai iya wanke kan shi ba, sai ya ce watakila an yi cushen ne a lokacin da yake jinyar rashin lafiya a asibiti.
Shugaban majalisar ya waiwayi Ali Ndume wanda shi ma ya nuna bai san da cushen ba.
A wata hira da aka yi da shi a BBC, Sanata Abdul Ningi ya yi ikirarin cewa kasafin kudi biyu ake amfani da su yau a gwamnatin tarayya.
...'Yan majalisar Kudu za su yunkuro
Bayan wannan zama sai wasu Sanatocin jihohin Kudu suka fara kokarin ganin yadda za su hana takwarorinsu tunbuke Akpabio.
Ningi ya ce sun dauko kwararru da suka duba kasafin kudin bana, a nan aka fahimci an yi wasu sauye-sauye a kan abin da aka sani.
Daga N25tr da majalisa ta amince da shi, Sanatan na Bauchi ya ce an yi karin N3tr don haka za su nemi zama da shugaba Bola Tinubu.
Bashi a kasafin kudin Najeriya
Kuna da labari kasafin 2023 da Mai girma Bola Ahmed Tinubu ya iske ya nuna 97% na kudin da aka samu ya tafi wajen biyan bashi.
Shugaba Bola Tinubu ya gaji tattalin arziki mai rauni, wanda dole yana bukatar garambawul kamar yadda masana suka shaida.
Asali: Legit.ng