"Saura Kiris Ku Ji Daɗi" Shugaba Tinubu Ya Aika Saƙo Ga Ƴan Najeriya, Ya Kaddamar da Sabon Shiri
- Bola Ahmed Tinubu ya ƙara kwantar da hankulan ƴan Najeriya game da wahalhalun da suka shiga na yunwa
- Shugaban ƙasar ya tabbatar da cewa gwamnatinsa za ta fito da ƙarin kayan abinci kuma nan bada daɗewa ba abubuwa za su fara kyau
- Ya ce gwamnatinsa ta shirya tallafawa mata domin suna daga cikin masu rauni da ke buƙatar a agaza masu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
FCT Abuja - Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya tabbatar wa ƴan Najeriya cewa nan bada jimawa ba abubuwa za su fara sauyawa zuwa abin farin ciki a Najeriya.
Shugaban ya ba da wannan tabbaci ne yayin da ƴan Najeriya ke fama da wahalhalun tsadar rayuwa sakamakon wasu sauye-sauyen gwamnati, The Cable ta rahoto.
Bola Tinubu ya ce yana sane da cewa ‘yan Najeriya na korafi kan yunwa, inda ya kara da cewa gwamnatinsa ta fito da kayan jin kai domin a magance illolin yunwa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shugaban ya kuma ce gwamnatinsa a shirye take ta aiwatar da sabon mafi karancin albashi, kamar yadda The Nation ta rahoto.
Tinubu ya kaddamar da sabon shiri na mata
Tinubu ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis, 7 ga watan Maris, a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja, yayin bikin kaddamar da shirin mata na Najeriya.
Ya ce:
"Gwamnatina za ta tafi da mata kuma wannan na ɗaya daga cikin tsare-tsarena, ina alfaharin tsayawa a gabanku yau kuma na fada muku cewa goben matan Najeriya za ta yi kyau.
"A matsayinmu na gwamnati aikinmu ne mu ba da fifiko ga ’yan ƙasa masu rauni waɗanda sune mata da kananan yara."
Yaushe ƴan Najeriya zasu samu sauƙi?
Da yake tsokaci kan halin yunwa da ake ciki, Shugaba Tinubu ya ce gwamnatinsa zata yi duk mai yiwuwa ta hanyar samar da tallafi domin al'umma su ci su ƙoshi.
"A yau ana nuna damuwa kan yunwa, za mu fito da kayan abinci domin kawar da duk wata illa ta yunwa, abubuwa sun yi wahala amma ba zamu zauna dindindin a haka ba.
"Nan bada daɗewa ba abubuwa za su fara canzawa saboda zamu fito da ƙarin abinci ga al'umma, sannan a shirye muke mu aiwatar da sabon mafi ƙarancin albashi."
- Bola Ahmed Tinubu
Gwamnatin Abba ta fara harin N10bn a wata
A wani rahoton, Gwamnatin Kano ta bayyana shirinta na ƙara yawan kuɗin shigar da take tarawa duk wata daga N2bn zuwa N10bn.
Shugaban hukumar tara kuɗin shiga ta Kano (KIRS), Sani Dambo, ne ya faɗi haka a wurin taron hukumar haraji karo na 154 a Abuja ranar Laraba.
Asali: Legit.ng