Majalisa Ta Lissafo Manyan Laifukan Mataimakin Gwamna da Ke Fuskantar Tsigewa, Ta Ba Shi Wa’adi
- Yayin da ake shirin tsige mataimakin gwamnan jihar Edo, Philip Shaibu, Majalisar jihar ta lissafo laifukan da Shaibu ya yi
- Majalisar a jiya Laraba 6 ga watan Maris ta fara shirin tsige mataimakin gwamnan kan zargin bankada sirrin gwamnatin jihar
- Har ila yau, Majalisar na zargin Shaibu wanda ya sha kaye a zaben fidda gwani da ba da shaidar karya a yayin rantsuwa a kotu
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Edo – Majalisar jihar Edo ta fara shirin tsige mataimakin gwamnan jihar, Philip Shaibu a jiya Laraba 6 ga watan Maris.
Majalisar na zargin Shaibu da bayar da shaidar karya da kuma cin amana wurin sakin bayanan sirri na gwamnatin jihar.
Menene dalilin shirin tsige Shaibu?
Shugaban masu rinjaye a Majalisar, Charity Aiguobarueghian shi ya bayyana shirin tsigewar a yayin zaman Majalisar, cewar Punch.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Mambobin Majalisar 21 daga cikin 24 ne suka sanya hannun amincewa da tsige Shaibu a korafin da aka gabatar a ranar 5 ga watan Maris.
Har ila yau, Kakakin Majalisar, Blessing Agbebaku wanda ya tabbatar da samun korafin ya umarci magatakarda ya fara gabatar da shirin tsige Shaibu.
Wa'adin da kakakin Majalisar ya bai wa Shaibu
Agbebaku ya bai wa mataimakin gwamnan kwanaki bakwai domin ya yi martani kan fara shirin tsige shi da ake yi a Majalisar, cewar TheCable.
Kokarin jin a bakin Shaibu ya ci tura yayin da ‘yan jaridu suka tuntubi hadiminsa a bangaren yada labarai, Musa Ebhomiana.
Wannan shirin tsige Shaibu na zuwa ne yayin da ake ci gaba da takun saka tsakanin mataimakin gwamnan da Gwamna Godwin Obaseki.
Hakan ya faru ne tun bayan sanar da muradin tsayawa takara da Shaibu ya yi a zaben gwamnan jihar da za a yi, cewar Daily Post.
Majalisar Edo ta fara tsige Shaibu
Kun ji cewa Majalisar jihar Edo ta fara shirin tsige mataimakin gwamnan jihar, Philip Shaibu a jiya Laraba.
Wannan na zuwa ne yayin da ake ci gaba da takun saka tsakanin mataimakin gwamnan da Gwamna Godwin Obaseki.
Tun bayan nuna sha’awar tsayawa takara da Shaibu ya yi a zaben da za a gudanar, aka fara samun matsala a tsakaninsu.
Asali: Legit.ng