Majalisa a Arewa Ta Fusata, Ta Tsige Manyan Masu Mukamai 2 da Dakatar da Ciyamomi 4, Ta Fadi Dalili
- Majalisar jihar Jigawa ta tsige wasu daga cikin manyan masu mukamai a Majalisar kan zargin hadin baki da cin amana
- Majalisar har ila yau, ta dakatar da ciyamomin kananan hukumomi hudu a jihar kan zargin badakalar kudade
- Majalisar ta dauki wannan matakin ne a yau Laraba 6 ga watan Maris bayan ta dawo daga hutun da ta yi
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Jigawa - Majalisar jihar Jigawa ta tsige manyan masu mukamai a Majalisar da kuma dakatar da ciyamomin kananan hukumomi hudu.
Majalisar ta dauki wannan matakin ne a yau Laraba 6 ga watan Maris bayan ta dawo daga hutu.
Wane zargi ake yi kan mambobin Majalisar?
Tsige masu mukaman a Majalisa ya biyo bayan kudirin da dan majalisar Hamza Ibrahim Adamu da ke wakiltar Malam Madori ya gabatar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Adamu ya na zargin wadanda da hadin baki wurin tsige kakakin Majalisar a kwanaki baya, cewar rahoton Tribune.
Kudirin ya samu karbuwa daga sauran mambobin Majalisar wanda ya yi sanadin tsige mataimakin shugaban masu rinjaye, Hon. Aliyu Ahmed da ke wakiltar Kirikassama.
Har ila yau, an tsige mai ladabtarwa a Majalisar, Hon. Dayyabu Shehu Kwalo da ke wakiltar mazabar Taura.
An dakatar da ciyamomi 4
Daga bisani Majalisar ta dakatar da wasu ciyamomin kananan hukumomi guda hudu kan zargin badakalar makudan kudade, cewar Daily Trust.
Wadanda abin ya shafa sun yi badakalar ce a kananan hukumomin da suke wakila kamar yadda ma’aikatar kananan hukumomi ta yi zargi.
Kananan hukumomin da abin ya shafa sun hada da na Gumel da Ringim da Auyo da kuma karamar hukumar Dutse.
Yayin da ya ke gabatar da korafin, shugaban kwamitin kananan hukumomin a Majalisar Hon. Aminu Zakara Tsibut ya ce sun bankado badakalar ce yayin ziyara kananan hukumomin jihar 27.
Wannan na daga cikin himmatuwar Majalisar domin ganin ta tabbatar da gaskiya da kuma sa’ido a kananan hukumomi da kuma jihar baki daya.
Kakakin Majalisa ya sha da kyar
Kun ji cewa kakakin Majalisar jihar Jigawa, Haruna Aliyu Dangyatin ya sha da kyar bayan Majalisar ta yi kokarin tsige shi.
Wannan na zuwa ne bayan wata tafiya da kakakin Majalisar ya yi zuwa kasar ketare tare da gwamnan jihar, Umar Namadi.
Asali: Legit.ng