Hotunan Yadda Dubban ’Yan Kano Suka Tarbi Gawuna Yayin Kai Ziyara a Karon Farko Bayan Mika Mulki
- Dan takarar gwamnan Kano a jam’iyyar APC, Nasiru Gawuna ya samu kai ziyara jihar tun bayan mika mulki ga Abba Kabir
- Dubban magoya baya ne suka taro dan takarar tun daga filin jirgin saman Malam Aminu Kano har zuwa gidansa a birnin
- Rahotanni sun tabbatar da cewa wannan shi ne karon farko da Gawuna ya zo jihar tun bayan mika ga sabuwar gwamnati
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Kano – Dandazon magoya bayan dan takarar gwamnan Kano a APC, Nasiru Gawuna sun tarbe shi a yau a jihar.
Daily Trust ta tattaro cewa wannan shi ne karon farko da Gawuna ya zo jihar tun bayan mika ga sabuwar gwamnati.
Yaushe Gawuna ya ziyarci Kano?
Gawuna ya isa jihar ne a yau Lahadi 3 ga watan Maris inda dubban magoya bayansa suka tarbe shi cikin farin ciki da doki.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Idan ba a mantaba, shugaban jam’iyyar APC, Umar Ganduje shi ma ya kawo ziyara jihar kano bayan rasa nasara a Kotun Koli, Vanguard ta tattaro.
Rahotanni sun tabbatar da cewa Gawuna ya samu tarbar dubban magoya bayan ne inda suka taro shi daga filin jirgin sama na Malam Aminu Kano.
Dan takarar gwamnan ya samu rakiyar ta su har zuwa gidansa da ke kan hanyar Miller a kwaryar Kano.
Yadda Gawuna ya samu tarba yayin ziyara a Kano
Majiyoyi sun tabbatar da cewa Gawuna ya zo jihar ce don ganawa da ‘yan uwa da kuma gaisuwar ban gajiya ga masoyansa.
Ga hotunan a kasa:
Wannan ziyara na Gawuna na zuwa ne yayin da ake cikin hatsaniyar tsakanin Gwamna Abba Kabir da hukumar Hisbah.
Daurawa ya bar kujerar Hisbah
A baya, kun ji cewa Shugaban Hukumar Hisbah, Sheikh Aminu Daurawa ya yi murabus daga kujerarsa a ranar Juma'a 1 ga watan Maris.
Malamin ya tabbatar da murabus din nasa a cikin wani faifan bidiyo daya fito inda ya ke nuna rashin jin dadinsa kan abubuwan da suke faruwa.
Wanann na zuwa ne bayan maganganu da Gwamna Abba Kabir ya yi kan hukumar Hisbah da ayyukansu.
Asali: Legit.ng