Hisbah Ta Gana da Gwamnan Kano da Daurawa, Akwai Yiwuwar ‘Jin Labari Mai Dadi’

Hisbah Ta Gana da Gwamnan Kano da Daurawa, Akwai Yiwuwar ‘Jin Labari Mai Dadi’

  • Gwamna Abba Kabir Yusuf ya yi zama na musamman da shugabannin hukumar Hisbah a kokarin lafar da kurar da ta tashi
  • Mataimakin kwamandan Hisbah a Kano, ya shaida cewa shaidan ne ya nemi shiga tsakani amma an yi nasarar taka wuyansa
  • Kalaman Dr. Mujahid Aminuddeen sun nuna babu mamaki sun shawo kan Sheikh Aminu Daurawa bayan sun zauna da shi

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Kano - Shugabannin hukumar Hisbah ta jihar Kano sun yi zama da Abba Kabir Yusuf a ranar Asabar bayan wasu abubuwan da suka faru.

An rahoto cewa Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya sanar da ajiye aikin shugabancin hukumar wanda hakan sam bai yi wa al’umma dadi ba.

Kara karanta wannan

Daurawa v Abba: Malamai da manya sun yi maganganu kan murabus din Shugaban Hisbah

Gwamnan Kano da Aminu Daurawa
Gwamnan Kano da Shugaban Hisbah Hoto: Abba Kabir Yusuf/Muhammad Aminu Ibrahim Daurawa
Asali: Facebook

Hisbah: Mataimakin Daurawa ya yi magana

Mataimakin Kwamandan Hisbah na jihar Kano, Dr. Mujahid Aminuddeen ya shaidawa gidan rediyon Freedom halin da ake ciki a jiya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bayan godiya ga Allah madaukakin Sarki SWT, Mujahid Aminuddeen ya yi bayanin yadda zamansu ta kasance da Gwamna Abba Kabir Yusuf.

Kamar yadda duk ‘Dan Adam bai cika goma, mataimakin Kwamandan ya ce Mai girma gwamna ya fada masu abubuwa masu taba zuciya.

Mujahid Aminuddeen ya nuna cewa zamansu da gwamna ya sa an fahimci abubuwa da kyau bayan sabanin da kalamansa suka jawo a baya.

Daurawa ya zauna da shugabannin Hisbah

Daga nan kuma sai shugabannin na Hisbah suka hadu da Aminu Ibrahim Daurawa wanda a ranar Juma’a ya sanar da cewa ya bar kujerarsa.

"Kwalliya za ta biya kudin sabulu, kuma da izinin Ubangiji an take wuyan shaidan,

Kara karanta wannan

"Allah ya sa malam ya hakura": Jigon APC ya magantu kan sabanin Daurawa da gwamnatin Kano

"wannan abu ne da ba mu so kullum a Kano, Kano gari ne na addini, gari ne na musulunci."
"Wannan aiki da ake yi domin a daga martabar Kano kuma a taimaki Mai girma gwamna ne. Jama’a za su ji albishir mai dadi idan Allah ya so."

- Dr. Mujahid Aminuddeen

Dawowar Daurawa ta raba mutane

Dama wasu sun bada shawara cewa Sheikh Daurawa ya hakura da batun murabus, ya cigaba da aikin Hisbah amma a kan sharadi.

Sai dai ‘yan siyasa irin Muaz Magaji sun kalli lamarin da wani idanu na dabam, suna jan kunnen Aminu Ibrahim Daurawa ya yi hattara.

Tsohon kwamishinan kuma jagora a APC ya rubuta a Facebook cewa malamin ya yi hattara da ‘yan siyasa, za su yaudare shi ne kurum.

A shafin Hisbah a Facebook, an rubuta ‘AlhamdulilLah’, ma’ana godiya ta tabbata ga Allah SWT bayan kiraye-kirayen malamai a kasar.

Kara karanta wannan

Hisbah Kano: Tsohon hadimin Buhari ya magantu kan murabus ɗin Sheikh Daurawa

Ajiye aikin Daurawa ya jawo magana

Jin cewa Sheikh Aminu Daurawa ya hakura da kujerar shugaban hukumar Hisbah ya jawo cece-kuce a Kano da kuma wajen jihar a Najeriya.

Ana da labari Bashir Ahmad ya ce kalaman Abba Kabir Yusuf kan aikin dakarun Hisbah tamkar cire zanin kwamadan ne cikin kasuwa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel