Bayan Matsalar da Aka Samu, APC Ta Bayyana Wanda Ya Lashe Tikitin Takarar Gwamna a Zaben 2024

Bayan Matsalar da Aka Samu, APC Ta Bayyana Wanda Ya Lashe Tikitin Takarar Gwamna a Zaben 2024

  • Jam'iyyar APC ta ayyana Sanatan Edo ta Tsakiya, Monday Okpebholo, a matsayin ɗan takararta a zaben gwamnan jihar Edo mai zuwa a 2024
  • Shugaban kwamitin zaben fidda gwani, Gwamna Bassey Otu, ya bayyana Okpebholo a matsayin wanda ya samu nasara da ƙuri'u 12,433
  • Sanatan na ɗaya daga cikin waɗanda suka lashe zaɓen fidda gwanin da aka yi a wurare daban-daban kafin daga bisani APC ta soke su

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Edo - Sanata Monday Okpebholo (Edo ta Tsakiya) ya lashe zaɓen fidda gwani na takarar gwamna a inuwar jam'iyyar All Progressive Congress (APC).

Shugaban kwamitin shirya zaɓen kuma gwamnan jihar Kuros Riba, Bassey Otu, ne ya bayyana haka bayan kammala tattara sakamako daga kananan hukumomi 18.

Kara karanta wannan

Mataimakin gwamna ya ƙara haddasa sabuwar rigima a jam'iyyar PDP kan muhimmin abu 1

APC ta kammala zaben fidda gwani.
Jam'iyyar APC ta sanar da sakamakon zaben fidda gwani na takarar gwamnan Edo Hoto: Senator Monday Okpebholo
Asali: Twitter

Taya aka zabi ɗan takarar gwamna a APC?

Jaridar The Nation ta tattaro cewa an tattara sakamakon tare da ayyana wanda ya samu nasara a Lushville Hotel and Suites yankin Gapiona Avenue a Anguwar GRA a Benin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanata Okpebholo ya samu ƙuri'u 12,433 wanda ya ba shi damar doke mamba mai wakiltar Ovia a majalisar wakilan tarayya, Dennis Idahosa, wanda ya samu ƙuri'u 6,541.

Idan baku manta ba APC ta tsaida ƴan takarar gwamna uku a zaɓen fidda gwanin da kwamitin Gwamna Hope Uzodinma na jihar Imo ya jagoranta ranar Asabar, 17 ga watan Fabrairu.

Yadda aka samu ƴan takara uku a zaben farko

Kwamitin Uzodinma ya bayyana ɗan majalisar tarayya, Dennis Idahosa a matsayin wanda ya samu nasara, rahoton The Cable.

Haka nan kuma baturen zaɓen ya ayyana Sanata Okpebholo a matsayin wanda ya ci zaɓen da aka gudanar da gidan tsohon ɗan takarar gwamnan jihar, Fasto Osagie Ize-Iyamu a Benin.

Kara karanta wannan

Mataimakin Shugaba Tinubu da gwamnoni 3 sun halarci jana'izar gwamnan APC da ya mutu a Owo

Duk dai a wannan rana, mai magana da yawun jami'an zaben kananan hukumomi, Ojo Babatunde, ya ce Anamero Sunday Dekeri, ne ya lashe zaɓen.

Lamarin ya jawo zanga-zanga kala daban-daban amma daga bisani uwar jam'iyya ta ƙasa ta sanar da soke zaɓen tare da kafa sabon kwamiti karƙashin Gwamna Otu.

Wanene ɗan takarar PDP a zaɓen Edo?

A wani rahoton kuma Jam'iyyar PDP ta bayyana sakamakon zaben fidda ɗan takarar gwamnan jihar Edo wanda aka yi ranar Alhamis, 22 ga watan Fabrairu, 2024.

Attajirin ɗan kasuwa kuma lauya, Asue Ighodalo, shi ne ya samu nasarar doke ƴan takara 9 ciki harda mataimakin gwamna, Philip Shaibu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262