'Yan Sanda Sun Kama Shugaban Jam'iyya Na Ƙasa Kan Muhimmin Abu, Bayanai Sun Fito
- Jami'an rundunar ƴan sanda sun kama shugaban Labour Party na ƙasa, Barista Julius Abure a Benin City, babban birnin jihar Edo ranar Laraba
- Duk da babu cikakken bayani kan kama shi a hukumance mma wasu hotuna sun nuna shi zaune a kasa kafin daga baya ƴan sanda su jefa shi mota
- Wannan na zuwa ne yayin da ake zargin Abure da yin sama da faɗi da makudan kuɗin da jam'iyyar LP ta tara lokacin zaben 2023
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Edo - Jami'an ƴan sanda cikin shirin aiki sun damke shugaban jam'iyyar Labour Party (LP) na ƙasa, Barista Julius Abure, ranar Laraba, 21 ga watan Fabrairu, 2024.
Jaridar Leadership ta tattaro cewa ana zargin Abure da yin sama da faɗi da makudan kuɗi da suka kai Naira biliyan uku mallakin jam'iyyar LP.
Har kawo yanzu da muke haɗa wannan rahoton babu cikakken bayani kan kama shugaban LP a Benin City, babban birnin jihar Edo.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sai dai wasu hotuna da suka bayyana a shafukan sada zumunta sun nuna Abure yana zaune a kasa kafin daga bisani 'yan sandan su dauke shi a cikin mota.
Meyasa jami'an tsaro suka kama shugaban LP?
A rahoton da Arise News ta wallafa a manhajar X, ƴan sanda sun kama Abure ne bisa zargin yunƙurin kisan kai.
Kuma an damƙe shi ne bayan tsohon shugaban matasan LP na ƙasa, Eragbe Anselm Aphimia, ya shigar da ƙorafi a kansa.
Legit Hausa ta fahimci cewa wannan lamarin na zuwa ne ƙasa da sa'o'i 24 gabanin zaɓen fidda ɗan takarar gwamnan jihar Edo na jam'iyyar LP.
A wani bidiyon nuna adawa da kama shugabansu, wasu mambobin LP sun ce sn kama Abure ne saboda jam'iyya mai mulki ta gano cewa Labour Party ce zaɓin al'imma.
Jam'iyyar All Progressive Congress (APC) ce ke mulkin ƙasa yayin da jam'iyyar PDP ke mulkin jihar Edo.
PDP na tsaka mai wuya kan kujerar sakatare
A wani rahoton kuma Jagororin jam'iyyar PDP na shiyyar Kudu maso Gabas sun bayyana wanda suke son ya gaji kujerar Sakatare duba da tsarin karɓa-karɓa da kundin tsarin doka.
Sun bayyana cewa Sanata Samuel Anyanwu ya yi murabus daga kujerar lokacin da ya nemi takarar gwamnan jihar Imo a zaben da ya wuce.
Asali: Legit.ng