Jam’iyyar APC Ta Shiga Rudani Bayan Ayyana Zaben Fidda Gwanin Edo ‘Inconclusive’, Ta Fadi Dalili
- Yayin da aka shiga rudani kan zaben fidda gwanin jihar Edo na jam’iyyar APC, Kwamitin jam’iyyar ya dauki mataki kan zaben
- APC ta dauki matakin ayyana zaben wanda bai kammala ba inda ta sake sanya ranar Alhamis 22 ga watan Faburairu don kammalawa
- Zaben wanda aka gudanar ya bar baya da kura inda aka samu ‘yan takarar gwamnan har mutum uku a matsayin ‘yan takara
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja – Jam’iyyar APC mai mulkin Najeriya ta ayyana zaben fidda gwanin jihar Edo wanda bai kammala ba.
Zaben wanda aka gudanar ya bar baya da kura inda aka samu ‘yan takarar gwamnan har mutum uku a zaben.
Mene dalilin rikici a zaben?
Yayin da shugaban kwamitin zaben, Gwamna Hope Uzodinma ya sanar da Dennis Idahosa wanda ya yi nasara, daga bisani an sanar da Monday Okpebholo shi ma ya yi nasara.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Har ila yau, Baturen zaben na kananan hukumomi, Ojo Babatunde ya kuma sanar da dan Majalisar Tarayya, Anaemero Sunday wanda ya yi nasara.
Wannan lamari ya jawo zanga-zanga a jihar musamman a sakatariya jam’iyyar inda suka nuna rashin jin dadinsu.
Martanin jam'iyyar APC kan lamarin
Yayin da ya ke jawabi ga jama’a, kakakin jam’iyyar ta kasa, Felix Morka ya ce kwamitin jam’iyyar ta yanke shawarar ayyana zaben wanda bai kammala ba.
Sanarwar ta ce:
“Kwamitin jam’iyyar ya yanke shawarar cewa zaben bai kammala ba kuma ya saka ranar Alhamis 22 ga watan Faburairu don karisa zaben fidda gwanin na APC.”
Har ila yau, ya ki amsa tambayoyi bayan sanar da wannan mataki da jam’iyyar ta dauka kan zaben.
Idahosa ya samu nasara
A baya, kun ji cewa dan Majalisar Tarayya a jihar Edo, Dennis Idahosa ya yi nasarar lashe zaben fidda gwani a jihar Edo.
Idahosa ya samu nasarar ce yayin zaben da aka gudanar don tsayar da dan takarar jam’iyyar APC a zaben jihar.
Gwamna Hope Uzodinma na jihar Imo wanda shi ne shugaban kwamitin zaben ya sanar da haka bayan kammala zaben.
Asali: Legit.ng