El-Rufai @ 64: Abin da Shugaba Tinubu Ya Fada a Kan Tsohon Gwamnan Kaduna
- Nasir El-Rufai ya cika shekaru 64 a duniya, masoya da abokan siyasa suna ta aiko masa da sakon murna a wannan lokaci
- Jawabi na musamman ya fito daga fadar shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya taya tsohon gwamnan Kaduna farin ciki
- Mai taimakawa shugaban Najeriya a kafofin sada zumunta, Olusegun Dada ya fitar da cikakken jawabin Bola Tinubu a X
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.
Kaduna - A rana irin ta 16 ga watan Fubrairun kowace shekara, ake taya Nasir El-Rufai murnar zagayowar ranar haihuwarsa.
Bola Ahmed Tinubu ya taya Malam Nasir El-Rufai murnar zagayowar wannan rana yayin da ya cika shekara 64 yanzu a duniya.
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya fitar da jawabi ta hannun Ajuri Ngalale yana yi wa tsohon gwamnan Kaduna fatan alheri.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tinubu ya taya Nasir El-Rufai murna
Mista Olusegun Dada ya wallafa jawabin shugaban kasa a dandalin X a ranar Asabar.
Mai girma shugaban Najeriyan ya yaba da rawar gani da gudumuwar da Nasir El-Rufai ya bada a duka mukaman da ya rike.
Tun daga lokacin da ya rike shugabancin hukumar BPE zuwa zamansa Ministan birnin Abuja, Tinubu ya ce El-Rufai ya yi fice.
Bayan nan ya ce Malam El-Rufai ya yi mulki na shekaru takwas a jere tun daga 2015 zuwa 2023 matsayin gwamna a Kaduna.
A tarihin Kaduna, Ahmad Muhammad Makarfi ne kurum ya dade haka a matsayin gwamna, shekaru kusan 16 da suka wuce.
Abin da Shugaba Tinubu ya fada a kan El-Rufai
"Bola Tinubu yana aika sakon murna ga tsohon gwamnan jihar Kaduna, Mallam Nasir Ahmad El-Rufai a lokacin murnar zagayowar ranar haihuwarsa a ranar 16 ga Fubrairu, 2024."
"Tinubu ya jinjinawa irin shugabanci da fitattun gudumuwar da kwararren shugaban ya nuna a kasar a tsawon rayuwarsa a aikin gwamnati a matsayin gwamna sau biyu a karkashin APC, tsohon Darekta Janar a BPE kuma tsohon Ministan harkokin Abuja."
- Ajuri Ngalale
A jawabinsa, shugaban Najeriyan ya nuna yana fata tsohon gwamnan zai cigaba da zama abin koyi ga ‘yan baya masu tasowa a yau.
Shugaba Tinubu ya yi wa tsohon sakataren na jam’iyyar APC mai mulki fatan koshin lafiya.
An hana El-Rufai Minista
A wani lamari mai kama da tuggun siyasa, ana da labarin yadda aka hana Malam Nasir El-Rufai sake zama Minista a gwamnatin nan.
Tun farko El-Rufai bai taba nuna kwadayin Bola Tinubu ya ba shi mukami ba, sai dai ma ya nuna ya fi sha'awar ya tsaya daga gefe guda.
Asali: Legit.ng