Gwamna Akeredolu zai biya tsofaffin Gwamnoni, Mataimakansu fanshon N10.916bn
-Gwamnatin Jihar Ondo za ta biya tsofaffin Gwamnoni fansho da giratuti a 2021
-An ware Naira biliyan 10 da za a ba tsofaffin gwamnonin Ondo da mataimakansa
-Gwamnan da ya fara shigo da wannan dokar a jihar ya rasu tun a shekarar 2007
A lokacin da gwamnati ta ke kukan karancin kudi, gwamnan jihar Ondo, ya sa fanshon tsofaffin gwamnoni da mataimakansu a kasafin kudin shekarar bana.
Jaridar Vanguard ta rahoto cewa gwamnatin jihar Ondo ta yi kasafin Naira biliyan 10.916 da za a biya tsofaffin gwamnoni da mataimakin gwamnoni a Ondo.
Gwamnatin Rotimi Akeredolu ta bayyana wannan ne a jiya ta bakin kwamishinansa na kasafin kudi da tsare-tsaren tattalin arziki, Mista Emmanuel Igbasun.
Emmanuel Igbasun ya bayyana haka a ranar Alhamis a garin Akure lokacin da yake bayanin abin da kasafin jihar na Naira biliyan 174 na shekarar nan ya kunsa.
KU KARANTA: Rundunar Amotekun ta hallaka mutum 11 a Jihar Oyo
Igbasun ya ce a 2021, akwai N10.916bn da aka ware za a biya wadanda su kayi mulki a jihar Ondo.
A jihohi da-dama, tsofaffin gwamnoni su kan tashi da makudan kudi a matsayin fansho, wasu gwamnoni sun fara zuwa majalisa domin soke wannan dokar.
Daga cikin tsofaffin gwamnoni da mataimakansu na jihar Ondo da ake sa ran za su fara amfana da wannan doka akwai Olusegun Mimiko da kuma Ali Olanusi.
Tsohon gwamna Marigayi Adebayo Adefarati ya shigo da wannan doka a lokacin da yake mulki a 2004.
KU KARANTA: Rikicin APC: "Gwamnan Kwara ya sa an tsige Shugaban Jam’iyya"
Jihohin da ake biyan tsofaffin gwamnoni su ne: Abia, Akwa Ibom, Bauchi, Anambra, Borno, Delta, Ebonyi, Edo, Gombe, Jigawa, Sokoto, Kano, da kuma jihar Kebbi.
Ragowar jihohin nan su ne: Kogi, Kwara, Imo, Neja, Ondo, Osun, Filato, Ondo, Ribas, Yobe.
Dazu kun ji labari cewa takarar babban jagoran jam'iyyar APC, Asiwaju Bola Tinubu ta samu gagarumin goyon baya daga wasu shugabannin majalisar dokoki.
Rahotanni sun bayyana cewa tsofaffin shugabannin majalisar dokoki masu-ci a yankin Kudu maso yammacin Najeriya, sun yi wa Bola Ahmed Tinubu mubaya’a.
Wadannan shugabannin majalisar dokoki su na so Tinubu ya yi takarar shugaban kasa a 2023.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng