Dan Takarar Gwamna a APC Ya Sake Janye Takara Ana Daf da Zabe, Ya Fadawa Ganduje Dalilansa
- Yayin da ake shirin gudanar da zaben fidda gwani a gobe Asabar 17 ga watan Faburairu, dan takarar APC ya sake janyewa
- Fasto Osagie Ize-Iyamu ya janye daga takarar ce a jam'iyyar APC a zaben da za a gudanar a watan Satumbar wannan shekara
- Wannan na zuwa ne bayan janyewa da wani dan takarar jam'iyyar APC ya yi a jiya saboda mutuwar dansa a kasar Amurka
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Edo - Kasa da awanni 24 kafin gudanar da zaben fidda gwani a jihar Edo, dan takarar gwamna a APC ya janye daga takara.
Fasto Osagie Ize-Iyamu ya janye takarar ce a zaben da za a gudanar a ranar 21 ga watan Satumbar wannan shekara.
Mene Ize-Iyamu ya ke cewa kan takarar?
Ize-Iyamu na daga cikin manya-manyan 'yan takarar jam'iyyar APC a zaben jihar wanda ya ke da magoya baya sosai, cewar Vanguard.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Osagie ya bayyana haka ne a yau Juma'a 16 ga watan Faburairu a cikin wata sanarwa ga 'yan jaridu.
Sanarwar janye takarar an yi ta ne ga shugaban jam'iyyar, Abdullahi ganduje da kuma na jihar, Emperor Jarret Tenebe.
Mene dalilan Ize-Iyamu?
Sanarwar ta ce:
"Watanni kadan da suka wuce na gana da 'yan uwa da abokan arziki da 'yan siyasa don shiga takara tare da ceto jihar Edo daga kangi.
"Duk da na samu damar tsayawar bayan tantance ni, ina mai bakin cikin sanar da ku janye takara ta, duk da babu dadi amma hakan ya zama dole bayan ganawa da 'yan uwa da abokan arziki.
"Na dauki wannan mataki ne don tabbatar da hadin kai da zaman lafiya yayin zaben da za a gudanar."
Ize-Iyamu ya kuma roki al'ummar jihar da su karbi matakin da ya dauka da kyakkyawan zato inda ya ce ya na tare da su, cewar The Nation.
Dan takarar APC ya janye
Kun ji cewa wani dan takarar APC a jihar Edo, Ehiozuwa Agbonayinma ya janye daga takara kan mutuwar dansa.
Dan takarar ya janye ne bayan mutuwar dansa mai suna, Osazuwa Michael a kasar Amurka.
Asali: Legit.ng